✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta tsawaita hutun Sallah

An tsawaita hutun domin ci gaba da shagulgulan Karamar Sallah.

Gwamnatin  Kano ta tsawaita hutun da ta bayar na Karamar Sallah domin ba wa al’ummar Musulmi damar ci gaba da shagulgulan sallar a Jihar.

Da farko an ware ranakun Laraba da Alhamis a matsayin hutu amma aka tsawaita zuwa Juma’a bayan an yi Sallah a ranar Alhamis.

Kwamishinan Yada Labaran Jihar Kano, Muhamamd Garba ya sanar a ranar Alhamis cewa yin hakan ya zama dole saboda ranar Laraba da tun farko aka bayar hutu ta zama ranar 30 na watan Ramadan.

Sanarwar ta mika sakon Gwamna Abdullahin Ganduje na fatan alheri ga al’ummar Jihar a yayin da suke ci ga da shagulgulan sallah, wanda ya bukace su da su yi amfani da bikin sallar wajen neman kusanci da Allah.

Ganduje ya kuma roki Kanawa da su yi amfani da musamman lokacin Sallar Juma’a wajen neman yin addu’o’in neman zaman lafiya da aminci a fadin Najeriya.