✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta ware asibitoci 509 domin rigakafin COVID-19

Rukunin farko na rigakafin guda 200,000 sun isa Jihar

Gwamnatin Kano ta karbi rigakafin cutar COVID-19 guda 209,520 wanda ta ce nan gaba za yi wa mutane shi a fadin Jihar.

Shugaban Kwamitin Yaki da COVID-19 a Jihar, Dokta Tijjani Hussini ya ce an ware cibiyoyin lafiya 509 da mutane za su rika karbar rigakafin wanda za a shekara biyu ana yi a matakai hudu a jihar.

“Za a yi rigakafin ne a matakai hudu: da farko za a yi wa jami’an lafiya masu aikin yaki da cutar; rukuni na biyu kuma sauran ma’aikatan lafiya da mutanen da shekarunsu suka haura 50; na uku kuma masu fama da rashin lafiya; sai ragowar mutane a matsayin rukuni na hudu,” inji shi.

Dokta Tijjani wanda ya ce an riga an kammala adana rigakafin samfurin AstraZeneca a Jihar, ya bukaci “jama’a da su yi rajistar karbar rigakafin COVID-19 saboda da Gwamnatin Tarayya ta samar da adadain da zai wadata a Jihar”.

Ya yi bayanin ne a taron wayar da kai da aka shirya wa kungiyoyin kare hakki da ‘yan Jarida wanda ya gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar.

Da yake bayani, Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce karbar rigakafin na COVID-19 zai karfafi kokarin da jihar ke yi na yakar cutar.