✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta yi barazanar soke zangon karatu na uku

Gwamnatin jihar Kano ta yi barazanar soke zangon karatu na uku.

Gwamnatin jihar Kano ta yi barazanar soke zangon karatu na uku matukar makarantu masu zaman kansu suka ki rage kudin makaranta da suke karba daga iyayen yara.

Gwamnatin dai ta bukaci makarantun su rage kudin da kimanin kaso 25 zuwa 30 cikin 100 na abunda suke karba kan kowanne dalibi.

Kwamishinan Ilimin Jihar Kano, Muhammad Sanusi Kiru ne ya  yi gargadin cikin wata sanarwa da ma’ikatar ta fitar a ranar Alhamis.

Ya kuma ce daga daya ga watan Nuwanba 2020, matsawar makaratu masu zaman kansu ba su amsa kiran gwamnati ba, to babu shakka babu shakka za ta dauki matakin soke zangon karatu na uku baki-daya.

Kiru ya ce daukar matakin ya zama dole ga ma’aikatarsa la’akari da halin matsin tattalin arziki da mutane ke fama da shi a sakamakon zaman gida da aka yi a lokacin annobar Corona, wanda hakan ya taba tattalin arzikin jama’a da dama.

Ya ce, “Mun kafa kwamatin wucin gadi da zai tattauna da masu makarantu masu zaman kansu, akan rage wani kaso na kudin makaranta.

“Yanzu haka akalla jihohi hudu zuwa biyar sun nemi bukatar a rage kudin makaranta ko a soke zangon karatu na uku.

“Idan haka ya kasance sabuwar shekara ta 2021 zata fara da sabon zangon karatu kenan,”

“Muna fata masu makarantu masu zaman kansu za su nuna irin jin dadinsu da irin hadin kai da gwamnati da jama’ar Kano suke ba su a koyaushe” kamar yadda ya bayyana,” inji kwamishinan.