✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta yi wa ‘yan jarida bita kan cutar coronavirus

A yayin da likafar cutar Coronavirus ke ci gaba da bunkasa a Najeriya, Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano ta shirya taron bita ga ‘yan jarida…

A yayin da likafar cutar Coronavirus ke ci gaba da bunkasa a Najeriya, Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano ta shirya taron bita ga ‘yan jarida don su taimaka wajen yaki da cutar a jihar.

Taron ya samu hadin guiwar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), inda aka gayyaci ‘yan jarida 30 don wayar musu da kai game da cutar.

Jami’in wayar da kan al’umma game da cutar a Kano Auwal Abdu Fagge ya ce “wannan bita an shirya ta ne saboda ‘ yan jarida, a matsayinsu na masu ruwa da tsaki a Kano wajen yaki da cutar COVID-19,” in ji Fagge.

Ya kara da cewa bitar na da muhimmanci, musamman duba da irin rawar da ‘yan jarida ke taka wa wajen yaki da cutar.

Fagge ya gargadi jama’ar jihar, cewa har yanzu cutar na nan, duba da yadda kullum ake kara samun wadanda suke kamuwa da ita.

Yayin da yake gabatar da wata mukala mai taken ‘Hanyoyin tattaunawa don yaki da Coronavirus’ ya ce cutar ta sake bulla a karo na biyu.

Sai dai wakilin WHO Ibrahim Bebeji, ya koka kan yadda wasu mutanen ba su gaskata cewar akwai cutar ba.

Fagge, ya shawarci mahalarta taron da su dage wajen maganin labarun bogi game da cutar ta Coronavirus.

Mahalarta taron, sun koka game da yadda wasu kwamitin gwamnatin ke hana samun wasu bayanai wanda hakan na kawo nakasu a aikinsu.

Sai dai wanda suka shirya taron sun yi alkawarin magance wannan matsalar.

A makon da ya gabata ne gwamantin Kano ta rufe makarantu, a wani mataki na dakile yaduwar cutar a jihar.

Cutar dai ta yi sanadin rasa rayukan mutane sama da 500 a jihar daga watan Afrilu zuwa Mayu, kamar yadda kwamitin yaki da cutar na fadar Shugaban Kasa ya tabbatar.