✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kano za ta kashe miliyan N500 don kawata gadar kasa

Gwamnatin ta ware kudaden don kawata gadar kasa da nufin hana mutane zubar da shara a nan.

Gwamnatin Jihar Kano ta ware Naira miliyan 525 domin kawata gadar kasa ta Tijjani Hashim da ke daura da Kofar Ruwa a kan titin zuwa Dawanau da ta dangana har zuwa Katsina.

Kwamashinan Yada Labarai, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan bayan kammala zaman Majalisar Zartarwar Jihar a ranar Alhamis, inda ya ce gwamnatin jihar za ta yi wa gadar kwalliya da duwatsu masu kyalli.

Kazalika, kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakin ne don rage yawan zubar da shara cikin gadar kasan.

Har wa yau, majalisar zartarwar ta amince a sake ba da kwangilar saka duwatsu masu kyalli don karfafa ginin gadar kasa da ke titin Panshekara zuwa Madobi a jihar, a kan Naira miliyan 65.7.

Sauran ayyukan da gwamnatin Kano za ta yi sun hada da biyan kudin makaranta da alawus na daliban jihar da gwamnatin jihar ke daukar nauyin karatunsu a kasar Indiya, inda za ta kashe Naira miliyan 25.5.

Gwamnatin ta sake ware Naira miliyan 32 don sauya jadawali da kuma ayyukan makarantun gwamnati zuwa na zamani, da kuma Naira miliyan 19 domin shirya wasanni na shekara-shekara da zummar tunawa da tsohon shugaban kasa, Janar Murtala Ramat Muhammad.

Sai dai matakin gwamnatin jihar, karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya jawo ce-ce-kuce da suka, musamman a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin babu bukatar kashe makudan kudaden don kawata gadojin kasan.