✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano za ta sauya wa Jami’ar Wudil suna

’Yan majalisar sun kada kuri’ar amincewa da bukatar ce bayan an kammala yi wa kudirin karatu na uku.

Gwamnatin Jihar Kano ta soma shirye-shiryen sauya wa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar da ke Wudil zuwa sunan Alhaji Aliko Dangote, hamshakin attajirin nan na jihar.

Wannan dai na zuwa ne yayin da Majalisar Dokokin Jihar ta amince da dokar wadda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da mata kudirin watannin baya.

A zaman majalisar na ranar Talata, wanda Shugabanta, Hamisu Chidari ya jagoranta, ’yan majalisar sun kada kuri’ar amincewa da sauya sunan makarantar zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote.

Ana iya tuna cewa, tun a watan Mayun da ya gabata ne Majalisar Zartarwa ta Jihar Kanon ta aika wa da Majalisar Dokokin wasikar wannan bukata.

Majalisar Zartarwar dai karkashin jagorancin Gwamna Ganduje ta nemi amincewar sauya sunan jami’ar zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote, ADUST, Wudil.

Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Labaran Madari na jam’iyyar APC da ke wakiltar Karamar Hukumar Warawa ne ya gabatar da kudirin amincewa da dokar, inda Nuhu Acika na jam’iyyar APC-da ke wakiltar Karamar Hukumar Wudil ya mara masa baya.

’Yan majalisar dai sun kada kuri’ar amincewa da bukatar ce bayan an kammala yi wa kudirin karatu na uku.

Shugaban Majalisar ya umurci Magatakardar Majalisar da ya mika wa gwamnan kudirin don domin sanya hannu.

A zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan zaman majalisar, Labaran Madari ya bayyana cewa amincewar tana da nasaba ne da nasarorin da Dangote ya samu da kuma gudunmawa marar misali da ya bai wa bangaren ilimi da ci gaban jihar da kasa baki daya.

A shekarar 2001 ce aka kirkiri jami’ar da sunan Jami’ar Kimiyya ta Kano, daga bisani kuma a shekarar 2005 aka sauya sunanta zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano.

Aliko Dangote dai shi ne Uban Jami’ar wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya nada a shekarar 2008, sannan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sabunta masa nadin a Nuwambar 2021.