✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Katsina ta bayar da hutun kwana 2 albarkacin ziyarar Buhari 

Gwamnatin ta bukaci jama'ar jihar su nuna wa Buhari da tawagarsa karamci a yayin ziyarar.

Gwamnatin Jihar Katsina ta ayyana ranakun Alhamis da Juma’a a matsayin hutu don bai wa ma’aikatan Jihar da na Kananan Hukumomi damar tarbar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar Al’adu da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Alhaji Sani Kabomo, ya raba wa manema labarai a ranar Laraba a Katsina.

Ana sa ran shugaba Buhari zai je Jihar ne domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Gwamna Aminu Bello Masari ta aiwatar.

Sanarwar ta bayyana cewa kwanakin aikin ba za su shafi ma’aikatan da ke cikin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, bankuna da masu samar da masu gudanar da wasu ayyukan na musamman ba.

Haka kuma ta bukaci ma’aikatan da abin ya shafa da sauran jama’a da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin tarbar Shugaba Buhari da mukarrabansa a Jihar.

Kabomo, ya kuma shawarci jama’ar Jihar da su nuna wa Buhari da ayarinsa karamci a matsayinsa na dan gida a yayin ziyarar.