✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kwara ta gargadi makarantu kan hana sanya Hijabi

Kada su kuskura su hana wa dalibansu mata Musulmai sanya hijabi a makaranta.

Gwamnatin Kwara ta yi gargadi ga makarantu da cewa kada su kuskura su hana wa dalibansu mata Musulmi sanya hijabi a makaranta.

Kwamishinar Ilimi da Bunkasa Rayuwa, Hajia Sa’adatu Madibbo Kawu, ita ce ta yi gargadin bayan wani sabon rikici da ya taso a kan neman tilasta wa dalibai Musulmi cire hijabinsu a makaranta.

“Tsarin Gwamnatin Jihar Kwara da ya ba wa dalibai Musulmi damar sanya hijabi a duk makarantun gwamnati, har da wadanda suke samun tallafi daga kasashen waje na nan tana aiki.

“Hakan kuma shi ne daidai da umarnin kotu da kuma abin da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadar,” inji ta.

Da take jawabi a wurin wani taron zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kiristoci da garin Ijabgo da ke Karamar Hukumar Oyun ta jihar, kwamishinar ta ce gwamnatin jihar ba za ta lamunci duk wani yunkuri na tayar da zaune tsaye a jihar ba.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne makarantar sakandaren Baptist High School da ke Ijagbo a Jihar Kwara ta hana wasu dalibanta shiga harabar makarantar saboda daliban sun ki su cire hijabansu.

Abin da makatantar ta yi wa daliban ya haifar da damuwa a jihar, musamman ganin cewa a shekarar da ta gabata rikici ya barke a jihar kan haramta wa dalibai Musulmi sanya hijabi a makarantu.