✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Legas za ta binciki yadda aka raba kyauta fetur a jarkoki a wajen biki

Lamarin na zuwa ne a lokacin da ake fama da wahalar mai a Najeriya.

Gwamnatin Jihar Legas ta sha alwashin bincikar wani faifan bidiyo da ya karade gari da ke nuna yadda ake raba kyautar man fetur a cikin jarkoki a wajen wani biki a jihar.

Kwamishinan Yada Labarai da Tsare-tsare na jihar, Mista Gbenga Omotosho ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

A cikin makon nan ne wata mata da aka bayyana sunanta da Chidinma Pearl ta dauki hankulan mutane musamman a kafafen sada zumunta na zamani, bayan ta yanke shawarar raba man fetur din a cikin jarkokin a matsayin kyauta a wajen bikin nata a yankin Erelu Okin.

Bidiyon dai ya nuna wasu jarkoki masu cin lita 10 da aka jejjera da man fetur a cikinsu, wadanda aka ajiye don raba wa wadanda suka zo wajen bikin nata.

Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan wahalar man fetur din da ta kai tsawon sama da mako uku.

Amma sanarwar Gwamnatin ta Legas ta ce, “Tabbas wannan abu ne mai matukar hatsari, kuma zai iya haddasa asarar rai da ta dukiya. Hakan ya kuma saba da kowane irin matakin kare lafiyar al’umma.

“Gwamnatin Jihar Legas, ta hanyar Hukumar Kula da Kiyaye Lafiyar Al’umma, za ta binciki lamarin tare da tabbatar da cewa dukkan mai hannu a ciki ya girbi abin da ya shuka.

“Kula da lafiya da dukiyoyin mazauna Legas da ma baki shi ne babban aikin gwamnatin Babajide Sanwo-Olu,” inji sanarwar.

’Yan Najeriya dai na ci gaba da fuskantar matsalar man fetur duk kuwa da alkawuran da gwamnati ta sha yi kan kawo karshen matsalar nan ba da jimawa ba.

Rahotanni dai na nuni da cewa wasu gidajen mai na sayar da man a kan kusan N250 kan kowace lita a wasu jihohin, lamarin da ya kai ga karin kudin sufuri.