✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Najeriya ta ba da hutun aiki ranar Alhamis

Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar Alhamis 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin murnar cikar Najeriya shekara 60 da samun ‘yanci. Ministan Harkokin…

Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar Alhamis 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin murnar cikar Najeriya shekara 60 da samun ‘yanci.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya sanar da hutun a madadin Gwamnatin Tarayya.

Ya taya daukacin al’ummar kasar murnar zagayowar ranar samun ‘yancin yayin da ya tunatar da jajircewar da Gwamnati ke y i wajen inganta jin dadin al’umma da bunkasa tattalin arziki.

Ministan wanda shi ne tsohon Gwamnan jihar Osun, ya ce cika shekaru 60 da samun ‘yanci lamari mai muhimmanci  sa yana kara tuni a kan yadda annobar coronavirus ta sanya dole a takaita shagulgulan da za a yi.