Gwamnatin Najeriya ta kara tsananta matakan yaki da cutar Coronavirus | Aminiya

Gwamnatin Najeriya ta kara tsananta matakan yaki da cutar Coronavirus

Boss Mustapha, Shugaban Kwamitin Yaki da cutar COVID-19 na Gwamnatin Tarayya.
Boss Mustapha, Shugaban Kwamitin Yaki da cutar COVID-19 na Gwamnatin Tarayya.
    Ishaq Isma’il Musa da Abbas Jimoh

Gwamnatin Tarayya a Najeriya ta sake tsawaita dokar hana baki daga kasashen Brazil, Indiya da Turkiyya shiga cikin kasarta zuwa wata guda a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar Coronavirus wadda ta yi kamari a cikin kasashen.

Haka kuma Gwamnatin ta sanya sunan Afirka ta Kudu cikin jerin kasashen da dokar ta shafa.

Wata sanarwa da Shugaban Kwamitin Yakin Cutar kuma Sakataren Gwamnatin Najeriya, Mista Boss Mustapha ya fitar a ranar Litinin, ta ce sabon matakin zai yi aiki na tsawon makonni hudu kafi a sake nazari a kansa.

Sakataren Gwamnatin ya ce suna ci gaba da lura kan abubuwan da ke faruwa a kasashen duniya dangane da abin da ya shafi cutar domin daukar matakan da suka dace na kare lafiyar ’yan Najeriya.

Ya kuma bai wa ’yan Najeriya shawarar ci gaba da sa ido gaya wajen daukar matakan kare lafiyarsu bisa la’akari da yadda  cutar annobar cutar ke ci gaba baza hajarta a wasu kasashen duniya.

Kazalika, ya kuma bayyana cewar suna mayar da hankali a kan batun samar da rigakafin cutar don ganin an yi wa jama’ar kasar da zummar kare kansu daga kamuwa da ita.

Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Mayun da ya gabata ne Gwamnatin Najeriya ta sanya wa wasu baki daga kashen Indiya, Brazil da kuma Turkiyya takunkumin shigowa cikin kasar duba da yadda cutar ta yi kamari a cikinsu.