Daily Trust Aminiya - Gwamnatin Neja na rokon ’yan bindiga su zo a yi sulhu
Subscribe

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello

Gwamnatin Neja na rokon ’yan bindiga su zo a yi sulhu

Gwamnatin Jihar Neja ta yi kira ga ’yan biniga a fadin jihar da su ajiye makamansu su rungumi tattaunawa da sasantawa don wanzar da zaman lafiya da tsaro.

Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane ya yi kiran ne yayin jawabi ga yan bindiga da jagororinsu da ke addabar jihar a Dutsen Magaji, Karamar Hukumar Mariga.

Ya kuma kirayi masu satar mutane da barayin shanu da su shiga cikin tattaunawar sulhun domin kawo karshen matsalolin tsaro da suka dabaibaye jihar tsawon shekaru.

Sannan ya bukaci jagororin nasu da su mara wa gwamnati baya don ganin an saki matafiyan da aka yi garkuwa da su a motar hayar Hukumar Sufuri ta Jihar Neja, daliban Kwalejin GSC Kagara.

Sakataren Gwamnatin ya ce gwamnati za ta ci gaba da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta hanyar inganta tsaro, don haka akwai bukatar mutane su hada kai da ita a kudirinta na kawar da duk wani laifi a jihar.

Sannan ya jaddada bukatar shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki da su dukufa kan yadda za a samu ’yan ta’adda, masu satar mutane, da barayin shanu su shiga cikin ayyukan samar da zaman lafiya na Gwamnatin.

Sheikh Gumi ya shiga tsakani

A nasa jawabin, sanannen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana kwarin gwiwar cewa tattaunawa da ‘yan bindiga zai kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a jihar da ma kasa baki daya.

Sheikh Gumi ya tunatar da su cewa Musulunci ya haramta kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, don haka ya yi kira gare su da su rungumi zaman lafiya ta hanyar ajiye makamansu.

Malamin shaida musu cewa zai ci gaba da tattaunawa da gwamnatin jihar don sama musu tallafi da nufin cimma burin da aka sanya a gaba.

Wasu daga cikin shugbannin ’yan bindigar yaba wa kokarin gwamnatin na wanzar da zaman lafiya.

Sun kuma jaddada cewa hakan zai taimaka wajen maido da zaman lafiya a fadin jihar.

Sun yi kira ga Gwamnatin da ta taimaka ta saki ’yan uwansu da jami’an tsaro ke tsare da su a fadin jihar.

More Stories