✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Oyo ta shirya zaman sulhu da bata-garin Jihar

Gwamnatin Jihar Oyo ta yanke shawarar yin sulhu da kungiyoyin matsafa

Gwamnatin Jihar Oyo ta ce za ta yi zaman tattaunawa da wasu bata-gari da kungiyoyin matsafa da na asiri a jihar domin wanzar da zaman lafiya da kawo karshen ayyukansu.

Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu da Yawon Bude Ido na Jihar Dokta Wasiu Olatunbosun ya bayyana haka ranar Alhamis, bayan wata ganawar sirri da ya yi da wakilan kungiyoyin.

Daga cikin wadanda aka yi ganawar da su a birnin Badun har da kungiyar OPC da ta ‘yan sintiri ta Najeriya (Vigilante Group of Nigeria) da sauransu.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar, da hadin gwiwar dukkanin kungiyoyin matasa masu amfani da makamai, ta kuduri aniyar kawo karshen tashe-tashen hankalin da ake yi da zubar da jini a tsakanin matasa ‘yan unguwa da kungiyoyin matsafa.

Ayyukan kungiyoyin asiri da fadace-fadace a tsakanin matasa a Jihar sun yi kaurin suna, lamarin da ke jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma masu tarin yawa.