✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Taliban na son kasashen Musulmi su goya mata baya

Gwamnatin ta Taliban na son kasashen Musulmi na duniya su tallafa mata.

Gwamnatin Taliban da ke mulki a kasar Afghanistan ta bukaci kasashen Musulmi da su kasance na farko da za su amince da ita, wanda hakan zai bai wa sauran kasashen duniya damar ci gaba da bai wa kasar taimakon da take bukata.

A 2020 Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Afghanistan na cikin hatsarin fuskantar tabarbarewar al’amura, muddin kasashen duniya suka gaza daukar matakan samar da hanyoyin samun kudaden shiga ga kasar.

Majalisar ta ce ya zama dole a tabbatar kudade sun ci gaba da gudana a Afghanistan duk da cewa ba a son hakan ya zama taimako kai-tsaye ga gwamnatin Taliban.

A wani taron manema labarai a ranar Laraba, Fira Ministan kasar, Mohammad Hassan Akhund, ya ce duk wani taimako da kasashen duniya za su bai wa Afghanistan ba aljihun ’yan Taliban zai shiga ba, sai dai domin amfanin al’ummar kasar.

Al’amura sun fara tabarbare wa Taliban a Afghanistan ne tun bayan da ta hambarar da gwamnatin kasar a watan Agustan 2021.

Taliban ta kafa dokoki da matakai masu tsauri ga al’ummar kasar, wanda hakan ya jefa mutane ciki tsaka mai wuya.

Wasu da dama sun fice daga kasar bayan fuskantar matsin lamba daga gwamnatin ta Taliban.