✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta bai wa ma’aikata hutu ranar Litinin

Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin, 3 ga watan Mayun 2021, a matsayin ranar hutu domin bikin zagayowar ranar ma’aikata ta duniya ta wannan shekarar. …

Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin, 3 ga watan Mayun 2021, a matsayin ranar hutu domin bikin zagayowar ranar ma’aikata ta duniya ta wannan shekarar. 

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Rauf Adesoji Aregbesola ne ya ayyana ranar a madadin gwamnatin tarayya a wata takarda da babban sakatare a ma’aikatar, Shuaib Belgore, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.

Ministan ya taya daukacin ma’aikatan Najeriya murnar sake ganin zagayowar wannan rana.

Tsohon gwamnan na jihar Osun kuma yaba wa ma’aikata kan hakuri da fahimta da ma goyan-bayan da suke bai wa tsare-tsaren gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a kokarinta ciyar da kasar gaba ta fuskar bunkasa tattalin arziki.

Kazalika, Aregbesola ya yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su ci gaba da sadaukarwa da nuna kishin kasa a dukkan al’amuransu.

Ya ce, “Gwamnati na daukar dukkan wasu matakai da suka dace na ganin an kawo karshen matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar nan.

“Muna kira da Kungiyoyin ma’aikata da masu kishin kasa da su yi iya bakin kokarinsu, su bayar da tasu gudunmawar wurin kawo karshen matsalar tsaro da ake fuskanta,” a cewarsa.