✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta sake gayyatar likitoci zaman sulhu

Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige ne zai jagorancin zaman da za a yi.

Gwamnatin Najeriya ta sake gayyatar likitoci zuwa teburin sulhu biyo bayan yajin aikin sai baba ta gani da suka tsunduma a makon nan.

Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige, ta hannun mai magana da yawunsa, Charles Akpan, ya ce zaman zai mai da hankali ne wajen rarrashin fusatattun likitoci bisa la’akari da yanayin da yajin aikin ya haifar a kasar.

Akpan, ya ce an kuma gayyaci ‘yan jarida yayin zaman sulhun da za a yi da misalin karfe 3.00 na Yammacin ranar Juma’a tsakanin Ministan da kuma kungiyar likitocin.

A yayin zaman, ana sa ran Shugaban Kungiyar Likitoci ta kasa (NARD), Dokta Uyilawa Okhuaihesuyi, zai jagorancin mambobin kungiyar, inda Dokta Ngige zai jagorancin bangaren Gwamnatin tarayya.

Idan ba a manta ba, tun a ranar 1 ga Afrilun 2021 ne likitocin suka tsunduma yajin aikin, wanda hakan ya jefa marasa lafiya da dama cikin tsaka mai wuta a Asibitoci.