✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya za ta fara aikin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano

A cewar ma'aikatar, aikin yana daga cikin irin yunkurin da gwamnatin ke yi na karade dukkan sassan Najeriya da layukan dogon.

Gwamnatin Tarayya ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara aikin titin jirgin kasa da zai taso daga birnin Ibadan na jihar Oyo zuwa jihar Kano.

Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya ce ta bayyana hakan a wasu jerin sakonni da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Lahadi.

A cewar ma’aikatar, aikin yana daga cikin irin yunkurin da gwamnatin ke yi na karade dukkan sassan Najeriya da layukan dogon.

Sanarwar ma’aikatar ta rawaito Ministan Sufuri na Najeriya, Chibuke Rotimi Amaechi yana cewa aikin zai kasance na hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin Najeriya da bankin China-Exim na kasar China.

Ya ce tuni Najeriya ta bayar da nata kason na aikin yayin da suka jiran bankin na China-Exim ya gabatar na nasa kafin a fara aikin gadan-gadan.

Ministan ya ba da tabbacin cewa ba za a sauya yadda aka tsara yin wannan layin dogon ba, kamar yadda aka sauya wanda aka yi tsakanin Legas da Ibadan.