✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Zamfara ta rufe Kasuwar Dansadau

An rufe kasuwanni hudu a Zamfara bayan hare-haren ’yan bindiga

Gwamnatin Jihar Zamfara ta rufe Kasuwar Dansadau da wasu kasuwanni uku saboda ayyukan ’yan bindiga da ke addabar Jihar.

Umarnin rufe kasuwannin ya fara aiki ne daga ranar Alhamis, 22 ga Afrilu, 2021, zuwa abin da hali ya yi; tare da umartar jami’an tsaro kar su raga wa masu saba dokar.

Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Ibrahim Dosara, ya ce kasuwannin su ne: Kasuwar Dansadau, a Karamar Hukumar Maru; Kasuwar Magami, a Karamar Hukumar Gusau; Kasuwar Wanke, Karamar Hukumar Gusau, da Kasuwar Dauran a Karamar Hukumar Zurmi.

“Gwamna Bello Mohammed Matawalle na cike da alhinin harin da aka kai wa al’ummomin yankin Magami na Karamar Hukumar Gusau ranar Laraba.

“Gwamnatin Jihar na takaicin hare-haren ta’addancin da ake kai wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, a yayin da suke neman halaliyarsu.

“Ta kuma yi tir da kashe-kashen da lalata dukiyar al’ummmoin da akasarinsu manoma ne, tare da mika ta’aziyya ga iyalan su suka yi rashi.

“Abin takaici ne faruwar wadannan hare-hare a daidai lokacin da gwamnati take kokarin samar da dawwamammen zaman lafiya a Jihar,” inji shi.

Sanarwar ta kuma umarci Ma’aikatar Agaji ta Jihar da ta gaggauta tantancewa tare da daukar bayanan asarar da aka yi, da kuma bayar da tallafi ga mutanen da suka yi asara.

“Tana kuma kira ga hukumomin tsaron da ke jihar da su hada kai da juna domin tabbatar da tsaro a fadin Jihar,” inji sanarwar.