✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Zamfara ta soke nadin sarautar kasurgumin dan bindiga, Ado Aleiro

Gwamnatin Zamfara ta dakatar da Sarkin da ya bai wa Aliero sarauta.

Gwamnatin Jihar Zamfara ta nesanta kanta da nadin sarautar da Sarkin ‘Yantodo na Karamar Hukumar Tsafe, Alhaji Aliyu Marafa ya yi wa kasurgumin dan bindigar da ake nema ruwa a jallo, Ado Aleiro a ranar Asabar.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe Sardauna, ya fitar a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce “Gwamnatin jihar Zamfara ta nesanta kanta daga nadin wani Sarkin fulani da Sarkin Birnin ‘Yandoto na Karamar Hukumar Tsafe yayi.

“Dangane da haka, gwamnan Jihar Bello Mohammed Matawalle, ya bayar da umarnin dakatar da Sarkin nan take.”

Kazalika, gwamnatin jihar ta kafa kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike game da dalilin da Sarkin na ‘Yantodo ya yi wa Aleiro sarautar Sarkin Fulanin yankin, duk da nemansa da ake yi kamar jamfa a Jos.

“Don haka ne gwamnan ya amince da kafa kwamitin da zai binciki lamarin da ya kai ga matakin da Sarkin ya dauka na yi masa nadin sarautar.

“Kwamitin da aka kafa mai mutum shida karkashin jagorancin Yahaya Chado Gora, ya kunshi mambobi da suka hada da Yahaya Mohd Kanoma da Muhd Umar B/Magaji da Lawal Abubakar Zannah da Isa Muhd ​​Moriki sai kuma Barista Musa Garba a matsayin sakatare.

“Sannan an nada Alhaji Mahe Garba Marafa, wanda shi ne Hakimin ‘Yandoto, a matsayin wanda zai ci gaba kula da harkokin masarautar.”

Aminiya ta rawaito yadda aka yi wa kasurgumin dan bindigar nadin sarautar gargajiya a ranar Asabar, lamarin da ya sa wasu da dama daga cikin ‘yan Najeriya ta da jijiyoyin wuya.