✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Zamfara ta umarci mutane su mallaki bindigogi

Matawalle ya ce a ba wa duk mai bukata lasisin mallakar bindiga domin kare kansa.

Gwamnatin Zamfara ta umarci al’ummar jihar su mallaki bindigogi domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da aka samu karuwarsu a daminar da muke ciki.

Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya umarci Kwamishinan ’Yan Sandan jihar ya ba da takardar izinin mallakar bindiga ga duk mai bukata a fadin jihar.

Kwamishinan Yada Labaran jihar, Ibrahim Magaji Dosara ya sanar cewa, “Gwamnati tana umartar jama’a da su tashi su mallaki bindigogi domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga.

“Ta kuma umarci Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara ya bayar da lasisin mallakar bindiga ga duk wanda ya cancanci ya mallaka domin kare kansa.

“Ta kuma kammala shirye-shiryen raba takardun neman izinin mallakar bindiga guda 500 ga kowacce daga cikin masarautu 19 da ke fadin jihar domin jama’a su samu su kare kansu.”

Sai dai ya bayyana cewa duk da haka dole sai masu neman lasisin mallakar bindigogi sun bi ta hannun Kwamishinan ’Yan Sanda.

Ya ce yin hakan ya zama dole sannan ya sanar da sauran matakan da gwamnatin ta dauka domin karya ayyukan ’yan bindiga da suka addabi jihar.

Ya ce “Sakamakon tabarbarewar tsaro a yankunan Mada da Wonaka da Ruwan Bore da ke Karamar Hukumar Gusau da kuma Masarautar Yansoto da ke Karamar Hukumar Tsafe, Gwamna  Matawalle ya rufe daukacin kasuwanni da wuraren sayar da dabbobi da ke wadannan wurare nan take, sai abin da hali ya yi.

“Ya kuma haramta hawa babur da sayar da man fetur nan take a yankunan da ka ambata — daga yanzu duk wani gidan mai da ke  yankunan an rufe shi.

“Duk wanda aka gani a kan babur kuma, to jami’an tsaro za su dauke shi a matsayin dan bindiga kuma ba za su saurara ba za su bude mishi wuta.

“Wannan kuma umarni ne ga jami’an tsaro da su tabbatar da cikakkiyar biyayya ga wannan doka, kada su raga wa masu taurin kai, amma gwamnati ba za ta lamunci kisan mutane haka kawai ba.”

Sauran matakan sun hada da daukar karin jami’an tsaron sa-kai na gwamnatin jihar guda 200 domin kara yawansu zuwa 500 a kowacce daga cikin masarautun jihar.

Dokar ta kuma tanadi kafa cibiya ta musamman domin tattara bayanan sirri kan masu yi wa ’yan bindiga leken asiri.

Sabuwar dokar ta yi gargadi kan bayar da bayanan karya kan masu yi wa ’yan bindiga leken asiri, domin duk wanda ya bayar da bayanan karya a kan masu yi wa ’yan bindiga leken asiri to hukuncinsa daya da su.

Don haka ta umarce su da su tabbatar da gaskiyar abin da za su kwarmata da duk wasu bayanan da za su ba wa jami’an tsaro.

Ta kuma bukaci Majalisar Dokoki ta jihar da ta gaggauta amincewa da dokar hukunta masu yi wa ’yan bindiga leken asiri da masu ba wa jami’an tsaro bayanan karya kan ’yan bindiga domin fara aiki da ita ba tare da bata lokaci ba.

Akwai kuma kwamitin tattara bayanan tsaro mai mutum 11 karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Kabiru Balarabe Sardau.

An kuma kafa wata runduna da za ta mara wa ’yan sa-kan gwamnatin jihar baya, karkashin jagorancin tsohon Kwamishinan ’Yan Sanda Mamman Anka da wasu kwamandoji bakwai da za su mara mishi baya.

An kuma dawo da kwamitin hukunta laifuka masu alaka da ayyukan ’yan bindiga na jihar karkashin jagorancin Dokta Sani Abdullahi Wanban Shinkafi da Antoni-Janar na jihar, Barista Aminu Junaidu Kaura a matsayin sakatare, da wasu mutum tara a matsayin mambobi.

Gwamnatin ta yaba wa bangarorin da suka ba da gudunmawa tare da mutunta sulhu da aka yi domin samun zaman lafiya a jihar sannan ta gargadi masu kawo wa sulhun cikas a yankunansu da su shiga taitayinsu.

Sannan ta umarci sojoji da ’yan sanda da sibil difens da sauran jami’an tsaro cewa nan take su je su rutsa ’yan bindigar a maboyarsu, har sai sun ga bayansu.