✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnoni 4 sun kaiwa Zulum ziyara jihar Borno

A ranar Laraba, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya Dokta Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya jagoranci tawagar wasu Gwamnoni zuwa ziyarar jaje da nuna goyon baya…

A ranar Laraba, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya Dokta Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya jagoranci tawagar wasu Gwamnoni zuwa ziyarar jaje da nuna goyon baya ga Gwamna Babagana Umara Zulum a game da harin da aka kaiwa tawagarsa a kan hanyar Baga, wanda a sanadiyarsa rayukan mutane sun salwanta.

Tawagar Gwamnonin ta kunshi na Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, da takwaransa na Filato, Simon lalong sai kuma na Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.

A jawabinsa, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Fayemi Kayode, ya bada tabbacin goyon dukkan Gwamnonin kasar nan, a kan samun zaman lafiya a jihar Borno da ma kasa baki daya.

Ya ce “hakika wannan abu da ya faru ga Zulum, ba wai gare shi bane kawai don mu ma ya shafe mu, kuma a kullum da abin muke kwana a ranmu.”

Ya mika sakon ta’aziyarsu dangane da rasuwar Shehun Bama da kuma Sarkin Biu, tare da sauran jama’ar da suka rasa rayukansu a harin da aka kaiwa tawagar Gwamna.

Tawagar Gwamnonin yayin tattauna wa a fadar Gwamnatin Borno

Dokta Kayode ya sha alwashin ba da gudunmawar Naira Miliyan 100 ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da ma al’ummar jihar Borno gaba daya.

A jawabinsa na godiya, Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana farin cikinsa ga kungiyar Gwamnonin a kan wannan ziyara da suka kawo masa.

Zulum ya ce babban dalilin da yasa gwamnatin jihar Borno ta kuduri aniyar mayar da jama’a garuruwansu shi ne “saboda halin rashin ayyukanyi, ba noma ga talauci a tsakanin alumma.”

Gwamnan ya kuma bukaci goyon bayan sauran Gwamnoni da su ci gaba da taimaka masa wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa jihar Borno da kasa baki daya.

“A madadin al’ummar jihar Borno muna mika godiyarmu ga wannan ziyara da Gwamnonin suka kawo, muna kuma yi musu addu’ar koma wa gida lafiya.”