✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin APC sun shiga taron gaggawa

Shugaban APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, kira aron ne kan wasu batutuwa masu alakala da yakin neman zaben na shugaban kasa da ’yan majalisar…

Gwamonin Jam’iyar APC mai mulkin Najeriya sun shiga taron gaggawa, kasa da mako guda kafin zaben shugaban kasa da ke tafe.

Shugaban APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, kira taron ne kan wasu batutuwa masu alakala da yakin neman zaben shugaban kasa da ’yan majalisar dokoki ta kasa da za a yi ranar Asabar.

Tun kafin fara taron sirrin, wanda ke gudana a Sakatariyar Jam’iyyar APC ta Kasa, an tsaurara jami’an tsaro a yankin.

Ganawar sirrin na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin gwamnonin APC suka bijire wa umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na haramta amfani da tsoffin takardun Naira 1,000 da N500.

Idan ba a manta ba, gwamnonin jihohi 12, ciki har da na APC sun maka Gwamnatin Shugaba Buhari a Kotun Koli suna neman kotun ta soke umarnin gwamnatin na haramta amfani da tsoffin takardun Naira 1,000 da N500.

Karin bayani na tafe.