✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnonin APC sun taya Buhari murnar cika shekaru 78 a duniya

Kungiyar gwamnonin da ke jagoranci karkashin jam’iyya mai mulki a Najeriya ta APC, sun taya Shugaba Muhammadu Buhari tare da iyalansa murnar cikarsa shekaru 78…

Kungiyar gwamnonin da ke jagoranci karkashin jam’iyya mai mulki a Najeriya ta APC, sun taya Shugaba Muhammadu Buhari tare da iyalansa murnar cikarsa shekaru 78 a duniya.

Shugaban Kungiyar, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi, a sakonsa na taya Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa, ya ce Shugaban Kasar ya dukufa wajen ganin ci gaban kasa da hadin kan ta.

Gwamnonin sun bayyana kwarin gwiwarsu gami da kyautata zaton cewa Najeriya za ta shawo kan matsaloloin tsaro da ta ke fuskanta a karkashin gwamnatin Shugaba Buhari.

“A yayin da muke maka barka da zagayowar ranar haihuwa da kuma nuna matukar godiya game da sadaukarwar da ka yi wa kasar mu, muna sake jaddada kudirin mu na yin aiki a karkashin jagorancin ka tare da yakini a kan cewa manufofin gwamnatin mu ta APC za ta cimma dukkanin tsammani da bukatun ’yan Najeriya.”

“Muna matukar alfahari da jagorancin ka mai cike da kishin kasa domin ka zama abin koyinmu kuma tushen karfafa mana gwiwa,” inji gwamnonin.