✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin Arewa maso Gabas sun yi ganawar sirri da Buhari

Suna ganawa da hafsoshin tsaro mako biyu bayan harin Boko Haram a kan gwamnan Borno

Gwamnonin Arewa maso Gabas sun yi ganawar sirri da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da manyan hafsoshin tsaro kan matsalar tsaro a yankin.

Ana fatar taron na sirri zai fi mayar da hankali ne kan matsalar rikicin Boko Haram da ya ki ci ya ki cinyewa a yankin tsawon shekara 11 da sauran matsalolin tsaro.

Ganawar tasu na zuwa ne kimanin mako biyu bayan mayakan Boko Haram sun kai wa Gwamnan Borno hari, lamarin da ya ja surutai da yin Allah-wadai.

Ministan Tsaro Bashir Magashi da ministan harkokin dan sanda, Muhammad Dingyadi da kuma shugabannin Yan Sanda da na hukumomin tsaro na DSS da NIA duk suna cikin taron.

Taron sirrin ya kuma samu halarcin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbaja da Mai ba da Shawara kan Tsaron Kasa Babagana Monguno da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Ibrahim Gambari.

A bangaren gwamnonin, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa ta Gabas Babagana Zulum na Jihar Borno ya jagoranci takwarorinsa na jihohin Taraba da Gombe da Bauchi da Gombe da Kuma Yobe zuwa tattaunawar.