✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnonin Arewa na nema wa sarakuna gurbi a gwamnati

Gwamnonin Arewa sun yi kwamiti kan yadda za a shigar da sarakuna cikin gudanar da gwamnati.

Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta kafa kwamitin sama wa sarakuna gurbi a dokar kasa da gudanarwar gwamnati.

Shugaban NGF, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato, ya ce hakan na daga cikin matsayar da kungiyar ta cimma a taron da ta yi a baya-bayan nan a Kaduna.

“Muna sane cewa kara wa sarakuna matsayi a gwamnatance na bukatar gyaran tsarin mulki, shi ya sa muka kafa kwamitin ya ba wa NGF shawara kan hanya mafi dacewa na cimma nasara”, inji shi.

Yakaddamar da kwamitin, Lalong ya ce sarakuna na taka muhimmiyar rawa a shugabanci duk da cewa dokar kasa ba ta ba su wannan matsayi ba.

Don haka ya bukaci kwamitin da ya kawo shawarwarin irin ayyukan sarakuna a yankin Arewa da ma daukacin Najeriya.

Kwamitin karkashin jagorancin Sakin Lafia, Mai Shari’a Sidi Mohammed Bage da sauran sarakuna daga jihohi Arewa 19 na da mako takwas ya kammala aikinsa.

Kwamitin zai mika rahotonsa ga Sanata Abdullahi Adamu, wakilin Majalisar Dattawa; Ministan Yada Labarai, Lai Mohamed, wakilin Majalisar Zartarwa ta Kasa; da kuma Hon. Usman Bello Kumo, wakilin Majalisar Wakilai.

A jawabinsa, shugaban kwamiti, Sarkin Lafia Mai Shari’a Sidi Mohammed Bage ya yaba da yunkurin na Kungiyar Gwamnonin Arewa sannan ya yi alkawarin mika rahoton kwamitin a kan kari.

A nasa jawabin lokacin taron kaddamarwan da ya gudana a Ma’aikatar Kananna Hukumomi da Masarautu ta jiharsa, Gwamna Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce kafa kwamitin zai sa a yi tafiya da manufa daya wurin inganta tsaro da jin dadin jama’a.