✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin Arewa sun yi daidai kan karba-karba a 2023 —Matasa

Sun ce babu yankin da ya iya ya yi wa Arewa barazana kan mulkin karba-karba.

Matasan yankin Arewa ta Tsakiya sun bayyana goyon bayansu ga matsayin da Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta dauka game da tsarin mulkin karba-karbar a zaben 2023 da kuma batun karbar harajin sayayya (VAT).

Idan ba a manta ba, Kungiyar Gwamnonin Kudu ta bukaci mulki ya koma yankinsu a zaben na 2023, suna kuma son a ba jihohi damar karbar harajin VAT.

Amma bayan wani taro da suka gudanar a Kaduna, gwamnonin jihoihin Arewa sun yi fatali da bukatar ta takwarorinsu nasu na Kudu, suna masu cewa Arewa ta fi karfin wani yanki ya fito yana mata barazana cewa dole ta bar mishi mulkin Najeriya da sunan karba-karba.

Ita ma Kungiyar Matasan Arewa ta Tsakiya, karkashin inuwar Dimokuradiyya da Hadin Kai, ta goyi bayan matsayin da gwamnomin Arewa suka dauka, cewa babu wanda ya isa ya yi wa Arewa muzurai don ta bar masa mulki.

Matasan sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabansu, Rabaran Joshua Maiwa’azi, bayan wani zama da suka yi a Abuja ranar Laraba.

Sanarwar bayan taron ta bukaci Shguaban Kungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, da ya ci gaba da tsayawa kai da fata wajen gabatar da Arewa a ko“ina a matsayin yanki daya dunkulalle mai hadin kai kuma mai alkibla daya.