✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin da suka sauya sheka sun ci amanar PDP —Wike

Ya ce sauyin shekar da wasu gwamnoni ke yi munafurci ne da cin amana.

Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, ya bayyana sauyin shekar da wasu takwarorinsa ke yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC a matsayin rashin tunani da cin amana.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a birnin Fatakwal ta hannu mai taimaka masa kan hanyoyin sadarwa, Kevin Ebiri, gwamnan ya ce yaudarace da munafurci ke sanya APC tana yi wa PDP kazafi da duk wata rufa-rufa da zummar janye ra’ayin mambobinsu.

A yayin da yake martani dangane kan sauyin shekar da Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar Talata, Wike ya bayyana lamarin a matsayin abun takaici kasancewar gwamnonin sun yi amfani da PDP wajen hawa karagar mulki kuma a karshe su juya mata baya.

A bayan nan an samu gwamnonin PDP uku da suka sauya sheka zuwa APC, lamarin da Gwamna Wike yake cewa “abin da jam’iyyar APC ke yi na kwashe ’ya’yan PDP cin amana ne bayan ta dade tana sukar magoya bayanmu a matsayin masu aikata laifuffuka.

“Gwamnonin da ke komawa APC a yanzu sun manta ko zabe basa iya lashewa sai amfani da kotuna wajen karbe kujerun da suka samu, yanzu kuma babu kunya sun wanke kafafu sun bar jam’iyyar da suka yi tsani da ita.

Gwamnan ya zargi gwamnatin APC na amfani da karfin mulki wajen tilastawa gwamnonin PDP ficewa daga cikinta, lamarin da ya ce wannan barazana ba za ta sa shi bari jam’iyyar PDP ba.

“Duk wani zargi ko kazafi da za a gabatar a kai na ba zai sa na sauya sheka ba, kuma ko da Jihar Ribas ce kadai za ta rage a cikin PDP a fadin Najeriya za su ci gaba da zama ba tare da wata fargaba ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, jam’iyyar PDP ta sha alwashin kalubalantar gwamnonin a Kotu da zummar ganin ta kwato kujerunta.