✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin Kudu maso Kudu na taro a Fatakwal

Tuni dai Gwamnonin suka hallara a Fatakwal domin taron.

Gwamnonin yankin Kudu maso Kudancin Najeriya na can suna gudanar da taro a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas ranar Litinin.

Taron wanda ya hadar dukkannin gwamnonin Jihohi shida da ke yankin, wanda su ka hada da na Akwa Ibom da Bayelsa da Delta da Kuros Riba da Ribas da kuma,  Rivers, da kuma Edo.

Wakilinmu ya rawaito cewa tuni Gwamnonin suka fara hallara a Fatakwal domin fara taron.

Kawo yanzu dai ba a san batutuwan da gwamnonin zasu tattauna ba.

Sai dai wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa ana harsashen Gwamnonin za su iya tattauna batutuwan da suka shafi dokar hana yawon kiwo, tsaro da kuma tattalin arzikin Jihohinsu.