Gyaran Gangar Auzunawa | Aminiya

Gyaran Gangar Auzunawa

     BALARABE LADAN balaladan@yahoo.com

A ranar Asabar din karshen makon jiya ne aka samu wani hadari a Kaduna sanadiyar fashewar tukunyar gas a wani wuri da ake sayar da iskar gas a Sabon Tasha da ke Kudancin garin Kaduna wanda ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane da dama.

Daga cikin wadanda suka rasu har da Shugaban Hukumar Makamashin Atom na Najeriya, Farfesa Simon P. Mallam da dansa, wadanda suke shagon wani mai aski lokacin da tunkunyar gas din ta fashe.

Wani mai gidan mai da ke kusa da wurin da hadarin ya faru ya bayyana wa wata jarida cewa ana kyautata zaton hadarin ya faru ne sakamakon amsa waya da matashin da ke aikin dura gas din ya yi a lokacin da yake dura gas din, wanda hakan ya sanya tunkunyar gas din ta yi bindiga.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa wadanda suka rasu sun kai mutum shida, ciki har da matashin da ke dura gas din.

Jami’in Hukumar Kula da Gidajen Sayar da Man Fetur da Dangoginsu (DPR) na shiyyar Kaduna, Isa Tanko, ya yi zargin cewa hadarin ya faru ne saboda amfani da tsoffin tukwanen gas da ake yi a wurin sayar da gas din, yana mai gargadin cewa hukumarsa ba za ta kyale mutane suna sayar da iskar gas ba bisa ka’ida ba.

A lokacin da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru  El-Rufa’i, ya ziyarci wurin da hadarin ya faru, ya bayar da sanarwar haramta sayar da iskar gas a wuraren zaman jama’a a fadin Jihar Kaduna, kuma haramcin ya fara aiki ne nan take.

Babu shakka akwai hadari a tattare da sayar da iskar gas a wuraren zaman jama’a, domin makamashi ne mai saurin kama wuta, dan tartsatsi kadan za a samu sai wuta ta tashi, sannan ga na’urorin zamani wadanda amfani da su a kusa da iskar gas din yana da hadari.

Sai dai kuma maimakon hana sayar da iskar gas din da kamata ya yi gwamnati ta yi nazarin hanyoyin da za a bi domin magance faruwar irin haka nan gaba, kamar horar da masu sayar da iskar gas din yadda ake sarrafa na’urorin dura gas din da yadda za su gane tukunya mai kyau da marar kyau da abubuwan da za su nisance su a lokacin da suke bakin aikinsu da kayayyakin da ya kamata su tanada domin kiyaye hadari da sauransu.

Sana’ar sayar da iskar gas din nan ta taimaka kwarai wajen samar da aikin yi ga matasa da kuma taimakawa wajen kare muhalli, domin yanzu mutane sun fara rungumar amfani da murhun gas sosai saboda yana da saukin harka, ga saurin biyan bukata, ga auki ga arha da saukin samu, saboda kusancin wuraren da ake sayarwa.

Idan aka ce duk masu sayar da iskar gas su koma bayan gari, za a koma gidan jiya ke nan, domin sai masu hali ne kawai za su iya zuwa nesa su sayo, talakawa marasa karfi wuraren sayarwar za su yi musu nisa, domin haka za su koma amfani da gawayi da itace, wadanda suke taimakawa wajen gurbata muhalli.

Ko a bayan gari ne ake sayar da iskar gas din kawai, hadari yana iya faruwa ya kashe mutane da dama, domin mutane masu saye suna taruwa da yawa a wurin sayarwar, ga kuma abubuwan hawa na masu saye an ajiye a kusa da na’urorin dura gas din.

Saboda haka ilimantar da masu sayarwa da kuma masu amfani da gas din ya kamata a mayar da hankali ba korar masu sayarwar ba. Tunda mutane sun fara gane amfani da iskar gas din, to sai a taimaka wajen samar da wuraren da za su rika saye a kusa da su ba tare da wahala ba.

Domin a yanzu haka akwai gidajen sayar da man fetur da dama a cikin wuraren zaman jama’a, amma saboda sun dauki matakan kare faruwa hadari ba a kore su ba. Haka ya kamata a yi wa masu sayar da iskar gas din, wato a tabbatar sun kware a harkar, sun san abubuwan da ke jawo hadari kuma sun tanadi kayayyakin da za su kare faruwarsa.

Amma hana sayar da iskar  gas a cikin mutane da gwamnatin Kaduna ta yi cikin gaggawa ba tare da ta zauna ta yi nazarin yadda za a taimaka wa masu saye su rika samu cikin sauki ba, kuma masu sayarwa su ci gaba da sana’arsu ba tare da sanya rayukansu da na sauran mutane a cikin hadari ba, a fahimtata kuskure ne babba, domin hakan zai iya haifar da wasu matsaloli masu yawa. Wato lamarin ya zama Gyaran Gangar Auzunawa ke nan, ana dinke nan, can yana fashewa.