✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gyaran gidan ajiyar namun daji zai lashe Naira miliyan 472

Gwamnan Jihar Ribas ya amince da kashe Naira miliyan 472 domin gyaran gidan ajiye namun daji na birnin Fatakwal wanda a da aka yi watsi…

Gwamnan Jihar Ribas ya amince da kashe Naira miliyan 472 domin gyaran gidan ajiye namun daji na birnin Fatakwal wanda a da aka yi watsi da shi.

Kungiyar Kula da Gidajen Ajiye Namun Daji da Wuraren Shakatawa ta Kasa (NAZAP) ita ce ta bayyana hakan a wata wasika da ta raba wa manema labarai a birnin Owerri na Jihar Imo.

NAZAP ta kuma yaba wa gwamnan saboda sake waiwayar gidan da ya yi wanda kafin yanzu ta ce ya kusa zama kango.

Ta kuma yi kira ga gwamnan da ya jajirce wajen ganin an gudanar da aiki mai inganci da kuma zai dace da yanayin dokoki da tanade-tanaden gidajen adana namun daji na kasa da kasa.

Daga nan kungiyar ta bukaci Gwamna Wike da ya jawo kwararru a jika yayin gudanar da aikin don ganin cewa an yi shi yadda ya kamata.

NAZAP ta yi gargadin cewa rashin yin hakan na iya jefa masu yawon bude ido, ma’aikatan gidan da kuma sauran jama’a cikin hadari.

“Ya kamata Gwamna ya san cewa akwai dokokin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya na hada kai da kungiyarmu da kuma tabbatar da cewa an tuntubi masana da kwararru wajen gudanar da aikin”, inji NAZAP.