✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gyaran matatun mai ya lashe N100bn a 2021 – NNPC

NNPC ya ce ya kashe makudan kudaden don inganta matatun man.

Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), ya ce ya kashezunzurutun kudi har Naira biliyan 100 wajen gyaran matatun mai na kasar nan a cikin shekarar 2021 da ta gabata.

NNPC ya bayyana hakan ne a cikin wani rahoton shekara da ya gabatar wa asusun hadaka na gwamnatin tarayya da Jihohi yayin wata ganawa.

Duk da cewa ba a bayyana matatun ba, NNPC ya ce ya kashe naira biliyan 8.3 a kowane wata na 2021 don gyara su.

Matatun man da ke karkashin kulawar NNPC sun hada da na Fatakwal da Kaduna da kuma Warri.

Baki dayansu, suna da karfin tace gangar mai 445,000 a kowacce rana, kuma duk da cewa Najeriya na da matatu hudu, tana fitar da danyen mai kasashen waje a tace sannan ta sayo tataccen don shigo da shi.

Hakan, a cewar NNPC ya sa Gwamnatin Tarayya narka makudan kudade wajen tace man tare da shigo da shi.

Lamarin da ya sanya gwamnatin shafe tsawon lokaci tana son janye tallafin da ta ke biya wa man fetur din.

Sai dai hakan ya jawo suka mai tarin yawa, inda masana harkar tattalin arziki ke ganin cewar janye tallafin na iya jefa talakawan kasar nan cikin mawuyacin hali da kuma tashin farashin kayan masarufi.