Haba manoman shinkafa! | Aminiya

Haba manoman shinkafa!

Wadansu manoma a gonar shinkafa
Wadansu manoma a gonar shinkafa
    Ado Saleh Kankiya

A bisa ga hobbasar da Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi bayan hawanta karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2015, na bunkasa noma, musamman na shinkafa da kuma niyyarta ta hana shigo da shinkafar  cikin kasar nan, ya sanya a cikin watan Nuwamban shekarar, Shugaba Buhari ya shugabanci kaddamar da wani gagarumin shirin noman shinkafa na kasa baki daya mai lakabin Anchor Borrower a Jihar Kebbi.

A karkashin shirin (wanda daga bisani ya game kasa a kan sauran cimaka), ana ba manoman shinkafar kasar nan bashin kayayyakin aikin noman shinkafa da kiyasinsu ya kama daga Naira dubu 160, zuwa Naira dubu 217, a kan kowace kadada daya, gwargwadon yawan kadadar da manomi zai noma ana kuma bukatar manomin ya biya daga shinkafar da ya noma.

Shirin na Anchor Borrower, wanda karkashin Babban Bankin Najeriya (CBN) ake gudanar da shi da farko gwamnatocin jihohi suka rika daukar wa manomansu lamuninsa, bayan wani lokaci Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN), a karkashin rassanta na jihohi da Abuja ta maye gurbin gwamnatocin jihohi wajen tsaya wa mambobinsu a kan lamunin.

Maganar nan da ake yi, bashin da Babban Bankin ya bayar ga ’ya’yan kungiyar RIFAN din ya kai Naira tiriliyan daya da biliyan daya  kuma ana ci gaba da bayarwa, don kuwa na samu labari a yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa daga Babban Bankin wajen raba bashin noman shinkafar ranin bana ga ’ya’yan Kungiyar RIFAN duk da taurin bashin da wadansu suke da shi.

Ka ma ce kwalliya tana biyan kudin sabulu a wannan shiri, fadi bata baki ne,  ganin gagarumar nasarar da aka samu cikin shirin noman shinkafar ya sanya a watan Agustan bara, Gwamnatin Tarayya ta rufe iyakokin kasar nan kuma daya daga cikin dalilan yin hakan da ta bayar har da tabbatar da kudirinta na tunda ta fara shirin inganta noman shinkafar na cewa kwaya daya ta shinkafar ba ta kara shigowa ba cikin kasar nan daga kasashen waje ba. Yanzu kuma a haka ake kai.

Sai dai kash! Kamar kowane shirin alheri da gwamnatoci kan yi a kasar nan, musamman don tallafa wa tattalin arzikin kasar da mutanenta, karshe sai a wayi gari ka tarar ba kasafai ba ’yan kasar da suka ci gajiyar irin wadannan shirye-shirye  ke saka wa kasar da mutanenta da alheri ba, ma’ana irin wadancan mutane sai su yi kememe, su ki biyan basussukan da aka ba su, bisa ga mummunar tarbiyyar da muka taso da ita ta kin biyan bashin gwamnati, har ka ji wadansu na cewa ai kayan gwamnati na kowa ne. Wa ya fada maka haka? Ba  daya daga cikin manyan addinan kasar nan biyu da ke koyar da wannan huduba, sai dai hububar Shaidan, ai biyan bashi ibada ne, sai kuma mai imani zai biya bashi.

Yanzu haka maganar da ake ciki, bayan daukar matakan matsin lamba a kan gwamnatocin jihohi da shugabannin Kungiyar RIFAN da Babban Banki ya fara, ya sanya gwamnatocin jihohi ta karkashin shugabannin rassan jihohi na Kungiyar RIFAN sun fara daukar matakan ganin ta kowane hali manoman shinkafar masu taurin bashin sun biya bashin.

Alal misali a Jihar Kano zuwa yanzu manoman shinkafa sama da dubu 200 suka amfana da bashin Naira biliyan 100  tun da aka fara shirin a shekarar 2017, kuma da kyar da jibin goshi zuwa yanzu manoman suka biya Naira biliyan daya da miliyan 200 kamar yadda Shugaban Kungiyar RIFAN, Alhaji Abubakar Haruna ya yi ikirari.

Tuni kungiyar ta fara gurfanar da irin wadancan manoma masu taurin bashi gaban kotu, inji shi.

Daga Jihar Kebbi kuwa inda shugaba Buhari ya fara kaddamar da shirin a shekarar 2015, Shugaban Kungiyar RIFAN reshen jihar,  Alhaji Muhammad Sahabi, manema labarai suka ruwaito yana cewa duk da irin alherin da manoman shinkafa a jihar suke samu tunda aka bullo da shirin, amma yanzu maganar da ake yi, manoman shinkafa dubu 70 da suka amfana da shirin, kuma suka yi biris da biyan bashin ake shirye-shiryen gurfanar da su a gaban kotu don ganin sun amayo bashin da suka karba.

Alhaji Sahabi ya bayyana mamakinsa kan yadda manoma 200 ne kacal suka biya bashin da ake binsu, duk da a fadarsa kafin fara shirin jihar tan dubu 70 na shinkafa kacal take nomawa duk shekara amma daga fara shirin a shekarar 2016, shinkafar ta karu zuwa tan miliyan daya da dubu 200. Yana mai tambayar wane dalili manomin shinkafa a jihar zai ki biyan bashin da aka ba shi?

A Jihar Kaduna ma kila sai alkali ya shiga tsakanin manoman shinkafar da Babban Bankin, don kuwa an jiwo shugaban kula da shirin da rarraba rancen da biyansa na jihar  Malam Hassan Tukur a garin Gwantu Hedkwatar Karamar Hukumar Sanga, yana aika sakon gargadi da jan kunne ga manoman shinkafar da suka ci bashin, suka kuma ki biya, kafin a kai ga gurfanar da su gaban kotu, cewa biyan bashin ya zama wajibi, ba wai ganin dama ba ne kamar yadda wadansu suke dauka.

A can Jihar Gombe a iya ce labarin taurin biyan bashin noman shinkafar ya dan sha bamban a kan na sauran jihohi, don kuwa an ruwaito Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafar kuma Shugaban Shirin Bayar da Rancen Noma na Jihar (NECAS), Alhaji Ahmad Muhammad Dukku, a kwanakin baya yana shaida wa manema labarai a Gombe babban birnin jihar cewa manoman shinkafa a jihar sai sam barka, domin a fadarsa a lokacin akwai kimanin buhu dubu uku na shinkafa da manoman suka kawo a zaman biyan bashin.

Ko kaffara ba zan yi ba, idan da bi za a yi daga jiha zuwa jiha a tsakanin jihohin kasar nan da suke cin gajiyar wannan lamuni na noman shinkafa da na sauran cimaka  kamar noman dawa da masara da rogo da sauransu na wannan gwamnati, to, da za ka tarar ba manoman jihar da za su fita kunya. Haka za mu zauna a kasa kowa kadan yake jira a kan damar da zai samu na dukiyar al’umma ta shiga hannunsa.

Kada Shaidan ya rika ribbatarmu, mu rika ganin kudin gwamnati namu ne don haka muna da damar mu ci su ta kowane hali Wallahi ba haka ba ne! Kai dai ka yi kokarin sauke nauyin amanar da ta hau kanka komai kankanta musamman ta dukiya, wajen  kokarin mayarwa.

Irin wannan hali ke dakushe ci gabanmu walau a daidaikunmu, ko a kungiyance ko a gwamnatance, har muke rasa ganin albarkar da muke nema.