✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Habasha na fama da matsananciyar yunwa da fari –MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ta ce yunwa da fari a kasar Habasa sun jefa miliyoyin ’yan kasar cikin mawuyacin hali. Rhotanni daga Habasha sun nuna…

Majalisar Dinkin Duniya ta ta ce yunwa da fari a kasar Habasa sun jefa miliyoyin ’yan kasar cikin mawuyacin hali.

Rhotanni daga Habasha sun nuna wannan shi ne fari mafi tsanani da kasar ta fuskanta cikin shekaru 40.

Lamarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya yunkurawa don kai tallafin jinkai a kasar inda take sa ran mutum miliyan 17 su amfana, kamar yadda  mai magana da yawun majalisar, Stephane Dujarric ya bayyana.

Dujarric ya shaida wa manema labarai ranar Laraba a New York cewa hakika, “Habasha na fuskantar wahalhalu wajen samun agaji,” daga mawuyacin halin da tsinci kanta.

Ya ce kawo yanzu mutum miliyan 24 ne suka samu tallafi a 2022 da suka hada da kayan abinci, kayan aikin noma, tsabtataccen ruwan sha da sauransu.

Ya kara da cewa, “Wasu sassan kasar na fuskantar hadarin ambaliya a ’yan makonni masu zuwa wanda ke iya shafar mutum sama da miliyan 1.7, ciki har da mata da kananan yara.”

A hannu guda, Sakataren Masalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya bayyana kaduwarsa kan yadda aka sake samun barkewarar tashin-tashina a wasu sassan kasar Habasha.

A kan haka ne ya yi kira da a dauki matakin gaggawa domin maido da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.