✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Habasha ta dakatar da bai wa ’yan Najeriya biza a kasarta

Dole masu zuwa Habasha daga Najeriya su sami biza daga Abuja.

Gwamnatin Habasha ta dauki matakin dakatar da bai wa ’yan Najeriya biza  bayan sun isa kasar.

Masu ruwa-da-tsaki na ganin cewa, matakin wanda ya fara aiki nan take, zai haifar da cikas ga sha’anin tafiye-tafiye zuwa kasar.

Tuni dai hukumar sufurin jiragen sama ta kasar ta sanar da abokan huldarta sabon matakin da aka dauka.

Cikin sanarwar da ya aike wa abokan kwasuwancinsa kamfanin Ethiopian Airlines ya ce, “ku sani daga yanzu an dakatar da bayar da biza ga ’yan Najeriya a kasar Habasha.”

Kamfanin Jiragen Kasar Habasa (Ethiopian Airlines) na daya daga cikin mashahuran jiragen sama na ketare da ke zirga-zirga a Najeriya.

Kafin wannan lokaci, fasinjojin da suka tafi Habasha daga Najeriya za su iya samun biza cikin sauki da zarar sun isa Babban Filin Jirgin Sama na Bole da ke Addis-Ababa, babban birnin kasar.

Amma da wannan sabuwar dokar, dole ne ga masu bukatar zuwa kasar daga Najeriya su mallaki bisar ET a ofishin jakadancin kasar da ke Abuja.