✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hadarin jirgin ruwa ya yi ajalin mutum 26 a Sakkwato

Gwanayen ninkaya sun tsamo gawawwaki mata 21 da kuma kananan yara biyar.

Hukumomi a Jihar Sakkwato sun tabbatar da mutuwar mutane 26 a sanadiyar wani hadarin jirgin ruwa da ya faru a yankin Karamar Hukumar Shagari.

Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Talata yayin da matafiyan ke kokarin tsallaka Kogin Shagari daura da garin Gidan-Maa-gana.

A zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN, Shugaban Karamar Hukumar Shagari, Alhaji Aliyu Dantani Shagari ya ce galibin wadanda suka rasun mata ne da kananan yara

Sai dai kawo yanzu ba a iya tantance ko mutane nawa ke cikin jirgin ba lokacin da ya kife don haka masu ninkaya ke can suna lalabe don tsamo karin gawawwaki ko kuma samun wanda ya tsira daga hadarin.

Ya ce ya zuwa yanzu dai an tsamo gawawwaki mata 21 da kuma kananan yara biyar da suka rasu a kifewar jirgin.

Hadarin jirgin ruwa dai ba bakon abu ba ne a wannan yankin kuma galibi a kan ta’allaka faruwarsa ga daukar mutane da kaya fiye da kima da rashin amfani da riguna kariya daga nutsewa da rashin kyawun yanayi da sauransu

BBC ya ruwaito cewa ko a watan Yunin bara ma mutane a kalla 13 ne suka rasa rayukansu a yankin na Shagari sakamakon kifewar da jirgin da suke tafiya a ciki ya yi lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga wani bukin aure.