✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 4 ’yan gida daya a Neja

’Yan gida dayan na daga cikin mutane bakwai da hadarin kwale-kwalen ya yi ajalinsu.

Wasu mutum hudu ’yan gida daya sun mutu sakamakon hadarin kwale-kwale a kauyen Zhigiri na Karamar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja.

Sanarwar da wata kungiya mai suna Coalition of Shiroro Association ta fitar ranar Talata ta tabbatar da faruwar lamarin.

Shugaban Kungiyar, Salis Mohamed Sabo ya ce mutum hudun ’yan gida dayan na daga cikin mutane bakwai da hadarin kwale-kwalen ya yi ajalinsu.

Sabo ya ce lamarin ya faru ne lokacin da mutanen suke kan hanyarsu ta zuwa kauyen Dnaweto domin halartar bikin radin suna da yammacin ranar Lahadi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa daga cikin wadanda suka mutu har da wani magidanci mai suna Mallam Mu’azu Babangida da wasu matansa guda biyu da kuma wani babban dansa guda daya.

A yayin da Sabo bai yi karin haske kan sauran mutanen da suka mutu ba, sai dai ya ce har yanzu akwai gawar mutum daya da aka nema aka rasa.