✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya yi ajalin mutum 1, 8 sun jikkata a hanyar Kano zuwa Zariya

Hadarin ya raunata 'yan gida daya mutum takwas.

Wani hadarin mota ya yi ajalin mutum daya tare da raunata mutum takwas ‘yan gida daya a kan hanyarsu daga Kano zuwa Zariya.

Aminiya tasamu cewa hadarin ya auku ne da misalin karfe 3:20 na Yammacin ranar Alhamis, inda ya ritsa da wasu iyalai yayin da suke tafiya zuwa Zariya daga Kano.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura FRSC na garin zariya, Hafiz Mohammed ya tabbatar da faruwar hadarin, wanda a cewarsa “Jami’anmu sun kai dauki wurin da hadarin ya faru.”

“Sun tabbatar da rasuwar namiji daya, sannan mutum takwas sun ji rauni,” kamar yadda ya bayyana.

Ya kara da cewa hadarin ya faru ne a daidai kauyen Dumbin Rauga da ke Zariya da wata mota kirar Toyota Hiace mai lambar KKR 100 XA.