✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya yi ajalin mutum 11 a Bauchi

An gargadi direbobi da su guji gudun tsere sa’a a yayin da shagulgulan karshen shekara suka gabato.

Mutane 11 ne suka mutu yayin da wasu su ka samu rauka daban-daban yayin da wata motar daukar kaya ta yi karo da ta fasinja a Jihar Bauchi.

Lamarin ya faru ne a kauyen Hawan Jaki a Alkaleri da ke hanyar Bauchi zuwa Gombe a ranar Asabar.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai a ranar Lahadi.

Mista Abdullahi ya bayyana cewa, motar fasinjan kirar Hiace ce mai lamba BA 114 A ta Hukumar Sufurin Jihar Bauchi, Yankari Express, da kuma tirela kirar DAF ta kamfanin Dangote mai lamba JMU 169 XA ne suka yi hadarin.

Abdullahi ya ce, jami’ansa sun isa wurin da hatsarin ya faru jim kadan da afkuwar sa, bayan da suka samu rahoto.

Sun kuma kwashe gawarwakin wadanda suka mutu zuwa Babban Asibitin Alkaleri, inda nan take likitoci suka tabbatar da mutuwar mutum tara yayin da biyu daga baya su ma suka ce ga garinku nan.

Kwamandan ya yi kira ga direbobi da su guji gudun tsere sa’a musamman a wannan lokaci na gabatowar shagulgulan bikin Kirsimeti da sabuwar shekara, inda yawan motoci ke karuwa a bisa hanyoyi.