✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadimai 120 sun yi min kadan —Shugaban karamar hukuma

Wani Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Nasarawa ya ce zai kara yawan hadimansa zuwa 200 zuwa 300. Alhaji Danlami Idris Odasko, wanda shi ne Shugaban…

Wani Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Nasarawa ya ce zai kara yawan hadimansa zuwa 200 zuwa 300.

Alhaji Danlami Idris Odasko, wanda shi ne Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa Eggon ya ce hadimai 120 masu rike da mukaman siyasa da ya nada su yi masa kada.

“Ina da masu rike da mukaman siyasa 120.

“Idan na samu karin kudadne shiga zan kara yawansu su kai 200 ko 300.

“Yawancinsu matasa ne da ke bukatar abun rayuwa na yau da kullum.

“Yin watsi da su ba zai haifar da da mai ido ba” inji odasko.

Ya ce matasan wadanda zababbun kansilolin karamar hukumar suka kawo na taka muhimmiyar rawa wajen aikin wayar da jama’a kan ayyuka da manufofin karamar hukumar.

Odasko ya ce N10,000 zuwa N20,000 da ake biyan hadiman nasa shi ne mafi a’ala da a bar su suna zaman kashe wando.