✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haduwar wakilinmu da Hausawan Nijar mazauna Abidjan

Tafiya Mabudin ilimi

Tafiya mabudin ilimi! Wannan karin magana ta yi tasiri kwarai a bulaguron da na yi zuwa Abidjan, babban birni kasar Cote d’Ivoire.

Kwana biyu kafin tafiyat tawa, na yi ta kokarin neman hanyar da zan samu haduwa da ’yan Najeriya mazauna Abidjan, amma hakan bai yiwu ba.

Haka ranar ta zo, jirginmu ya tashi a tashar jirgi ta Nnamdi Azikwe da ke Abuja da misalin karfe 10:50 na safe, muka kuma sauka filin jirgin F Houphouet Boigny da ke Abidjan.

Wani mai tura baro a gaban wani shago a birnin Abidjan. (Hoto: Moustapha Kadi)

Kafin mu yi nisa, Gidauniyar Malaman Afirka ta Sarki Mohammed na kasar Moroko (Mohammed VI Foundation of African Oulema) ce ta dauki nauyin tafiyar tamu domin halartar wani taron tattaunawa tsakanin masana da masu bincike kan addinai mabambanta.

Akalla mutum 600 ne daga kasashe 34 na Afirka suka halarci taron inda kowanne ya bada gudunmuwarsa kan hanyoyin da za a bi don tabbatar da zaman lafiya tsakanin addinai da kuma kauce wa ta’addanci.

Bayan kwashe kwana uku ana tattaunawa, an dauki wasu kwanaki ana gudanar da addu’o’i da ziyartar malaman addini da ke raye da wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

Hakan bai sakan mini marar shiga cikin gari ba domin zakulo amsar wasu tambayoyi da na tafi da su, musamman la’akari da gargadin da aka yi mani cewa an kama mana masauki ne a cikin filin jirgi saboda tsoron matsalar tsaro a kasar.

Kwana biyu kafin dawota, na nemi alfarmar zuwa domin haduwa da Jakadan Najeriya a Moroko, daga can ne na shiga kasuwa neman ’yan Najeriya da zan samu yin hira da su.

Duk da haka, abin ya ci tura, duk inda na je sai na tarar da ’yan kasar Jamhuriyar Nijar, musamman a shaguna da wuraren da ake gudanar da kananan sana’oi a garin.

Kayan wayar wasu kananan ’yan kasuwa a Abidjan. (Hoto: Moustapha Kadi)

Abin da ya fara jan hakali na shi ne, na zo wucewa cikin babbar kasuwar gari, sai na ji wani mai tallar soson wanka yana wa dan uwansa ba’a cewa, “Kai sakarai, ga babban mutum nan zai wuce kana ta bin matan da ba sayen kayanka za su yi ba. Ka yi masa talla!”

Da jin haka sai na juyo, na ce: “Kai malam bahaushe, me kake yi a Abidjan?”

Cikin murmushi ya kalle ni ya ce, “Ai daga ganin shigarka na tabbata kana jin Hausa.”

Labarin yadda Amadu ya zo Abidjan abin dariya ne da wauta, saboda a cewarsa, ya baro kasar Nijar ce domin ya yi kudi, amma ya kare a tallar soson wanka da matajn kai.

“Yanzu haka gida nake son na koma amma kuma ko na je, na riga na rabu da tsohuwar sana’ar da nake yi a gida.”

(Hoto: Moustapha Kadi)

Sai dai, Malam Lawali, mai shagon sayar da jikka da tufafi, ya bayyana wa wakilinmu cewa shi dan asalin Tawa ne a kasar Jamhuriyar Nijar, kuma yana jin dadin sana’arsa a Abidjan.

Ya kuma ce ya kwashe akalla shekara 20 a garin Abidjan.

“Ta mota muka zo, daga Niamey muka shiga Burkina [Faso] kafin muka zo Abidjan. Tafiyar akwai wahala amma mutanenmu da yawa suna nan suna kasuwanci,” inji shi.

Da na tambaye shi maganar ’yan Najeriya mazauna Abidjan, sai ya ce ba a cika samun Hausawa ba sai Yarbawa da ’yan kabilar Igbo masu sayar da kayan mota.

“Yanzu kaga a layin nan dukanmu hausawa ne ’yan kasar Nijar, amma babu dan Najeriya ko mutum daya,” inji shi.

Ya ce hakan yana da nasaba da bambancin yare da ke tsakanin kasashen da ke Turanci Ingilishi da Faransaci. 

Ya ce hakan yana da nasaba da rashin zuwansu Abidjan.

(Hoto: Moustapha Kadi)

A dan zaman da na yi a Abidjan, kadan ya rage na zama kurma, saboda rashin fahimtar yaren da ake yi.

Taron da muka halarta, tun daga farkonsa har zuwa karshe da Faransanci aka gudanar da shi, sai dai na saurari fassara, wanda akasari ba gamsashiyyar fassara ce ba.

Hakan nan kuma duk wanda ka tunkara ku yi magana da shi sai ya ce maka, “No English” ko “Little English” ballantana Hausa.

Musamman lokacin da na fito daga otel zan je Ofishin Jakadancin Najeriya, sai da na kira wani abokina da ke jin Faransaci a Najeriya ya yi mani tafinta kafin muka fahimci juna yadda ya kamata.

Duk da haka, na yi abokai da muke ingausar Turanci da Faransaci da kuma yaren bebaye.

Kadan daga cikin abin da yake cewa idan muna zaune a zauren tarbar baki shi ne, ‘go room’ sai ya nuna sama,  wato zai tafi dakinsa a saman bene ke nan.

Daga karshe, abin da ya fi yi mani ciwo shi ne kudadena N79,000 da jami’an gwamnatin Najeriya suka karbe a filin jirgi.

(Hoto: Moustapha Kadi)

Daga saukata suka ce sai na cika wata takarda mai suna “Travel Approval Form” wadda a cikinta suka sa biyan N39,500 na gwajin COVID -19 ga duk wanda zai shigo kasar bayan kudin da mutum ya kashe wajen yin sa a kasar da ya baro; Sai kuma karin N39,500 ga wanda bai kammala karbar allurar riga-kafin cutar ba.

A duk kasashen da na je, idan ka yi gwajin COVID-19  a Najeriya suna amincewa da sakamakon, inda kuma ba su aminta ba sukan yi maka gwajin ne a kyauta.

Amma a Najeriya, za su karbi kudinka, su bar ka ka shiga cikin kasar ba tare da sun gudanar da gwajen a filin jirgin ba. Wato ko kana dauke da cutar in dai har sun karbi kudin, to babu shi ke nan – in ya so kaje ka yada ta.

Kuma da yawa daga cikin wadanda suke dawowa Najeriya daga wasu kasashe sun tabbatar mani cewa ba sa zuwa a yi musu gwajin.