✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Haduwar ’yan Kannywood da ’yan BBNaija ta bar baya da kura

’Yan Kannywood sun yi wa juna wankin babban bargo a kafafen sada zumunta.

A makon jiya ne wanda na lashe gasar BBNaija na bana, Hazel Oyeze Onou, wanda aka fi sani da White Money, da wadda ta zo ta biyu, wato Roseline Afije, wadda aka fi sani da  Liquorose, suka amsa gayyatar gidan talabijin na African Magic a Jihar Kano.

Domin karramar ziyarar bakin, hukumar gidan talabijin din ta gayyaci ’yan Kannywood domin tarbar bakin da suka shigo Kano.

Daga cikin wadanda suka tarbe su, akwai Ali Nuhu da Adam A. Zango da Furodusa Alhaji Sheshe da Abubakar Bashir Maishadda da Naziru Dan Hajiya da Yakubu Muhammad da sauransu.

’Yan Kannywood din sun ta sanya hotunansu tare da bakin a shafukansu na sada zumunta suna murna da annashuwa.

Sai dai jim kadan bayan hotunan sun yadu a kafofin sadarwa, sai maganganu suka fara fita.

– Abin da ya jawo surutai –

– Shishshigi —inji Hadiza Gabon

Furodusa Naziru Dan Hajiya ya sanya hotunan bakin, inda ya yi yabo mai ga wanda ya zo na dayan.

A kasan rubutun nasa ne jaruma Hadiza Gabon ta ce, “Da haka kuke zuga na ku da kam.. bari dai in yi shiru dai. Shisshigi”

Sai Uzee Usman ya amsa mata da cewa, “Ashe kin gane”.

Nan Naziru ya dawo, ya mayar wa Hadiza Gabon martani cewa, “Amma kin san ina zuga ki.”

Amma ta ce mishi, “Ni ba na bukatar zugi kawai shisshiginku ke ban dariya,” inji ta; shi kuma Uzee Usman ta ce mishi, “To na ga Kannywood sun dage shi ya sa na ce su kan nasu suke wannan dagiyar da ba haka ba.”

Shi kuma Nasiru Ali Koki sai ya ce, “Shi kuma wannan wa ye?” Shi ma Rabiu Rikadawa, ya ce, “Ashe kuma an yi bako?”

– Auwal Isa West ya caccaki Hadiza Gabon –

A wani bidiyo da Aminiya ta gani, Auwal Isah West ya fito ya caccaki Hadiza Gabon, cewa ta raina mutanen da suka taimake ta.

“Hadiza da kike cewa da haka ake daga namu,  ki fada mana wani jarumi namu ko mace ko namiji da wani [abu] ya same shi ko na murna ko na jaje da ba a taya shi ba.

“Ke da kike wannan maganar, rashin sanin girman na gaba da ke ne.

“Kar ki manta lokacin da kika zo Jos daga Kaduna, lokacin da Yakubu Lere ya turo Jamilu Kochila ya kawo mana aikin ‘Bana Bakwai’ na farko, ko Hausa ba ki iya ba aka kawo ki za ki yi scene daya za ki fito a ’yar jarida.

“Daya cikin mutanen da kika ce ba sa daga nasu, shi ne ya sa ki a fim, wasu kuma a cikinsu suka saka ki a fim duniya ta san ki, amma yau ke ce kike da bakin magana saboda yawancin mutanenmu butulu ne ku ba ku san abin da ke damun ku ba, da kun ci abinci kun koshi, sai ku hau social media kuna fada wa mutane magana.

“Da shi ma wancan din wanda ba mu san ina ya sa gaba, Musulmi ne ko Kirista, shi wancan kawalin naku na Abuja da yake cewa ki kara ‘volume’. Shi ma ya san kan shi da shi nake magana. Ba na tsoron kowa,” inji shi.

A cikin maganar ya kara da cewa ba wai ’yan Kannywood ba ne suka nemi zama da baki, gayyatar su aka yi su ma, suka amsa.

– Auwal West ya ba Hadiza Gabon hakuri  –

Daga baya, Auwal Isa West ya sake yin wani bidiyon, inda ya nemi afuwar jarumar.

“A cikin maganganun da na yi, babu kamar kalma da na fada na zancen kawalinta.

“Wallah ban san wannan maganar ba, bacin rai ne ya kawo haka. Amma ina ba iyayenta da ’yan uwanta da masoyanta hakuri.

“Na yi ba daidai ba, amma don Allah ta yi hakuri. Na gode,” a cewarsa.

– Alhaji Sheshe ya bara –

Can sai ga furodusa Alhaji Sheshe ya sako dogon rubutu, inda ya ce, “Furodusa Alhaji Sheshe tare da na daya daga cikin mutanen da suka shiga gidan Big Brother white money.

“Dan asalin Jihar Kano ne kuma ya samu lambar yabo a wajenmu wajen yadda ya girmama Kannywood da mutanen cikinta.

“Dalilin da ya sa na ga ya burge ni ke nan saboda ya nuna muhimmanchin masana’antar shirya fina-finai ta Hausa da kuma yadda ya nuna jaruman fim din Hausa suna burge shi har ya kawo misali da daya daga cikin jarumanmu a wata hira da ya yi a cikin gidan Big Brother din.”

– Abin da ya kawo su Kano –

Alhaji Sheshe ya kara da cewa, “Haka ya sa bayan fitowarsu daga gidan sai shugabannin gidan talabijin na African Magic suka shirya wata muhimmiyar ganawa da masu ruwa da tsaki na Masana’antar Kannywood tare da shi wannan mutumun da ya zo na daya don nuna wa duniya muhimmanchin Kannywood da kuma kulla alakar ci gaba da cinikayya a tsakaninmu.”

– ‘Abin da ya ba ni mamaki’- 

A cewarsa, “Babban abin da ya fi ba ni mamaki da na ga wasu mutane daga cikin masana’antar Kannywood suna cewa mun yi shisshigi, wasu kuma suna cewa an yi hoto ba su saka a shafinsu ba.

“To dama an fada muku mun yi hoto ne don su dora a shafinsu? Mutanen nan fa zuwa suka yi suka gaishe mu suka kuma girmama mu sannan suka girmama masana’antarmu, suka kuma kara ba mu hadin kai don mu ci gaba da cinikayya a tsakaninmu da su.”

– Rashin sanin darajar Kannywood – 

“A cikin maganganunku akwai nau’ukan rashin sanin muhimmanchin sana’ar fim sannan akwai nau’in hassada akwai kuma nau’in rashin sanin muhimmancin daukaka.

“Ban ji mamaki ba ganin yadda wani kawali ya yi wani rubutu.

“Dama ai mun san ba sana’a ce ta kawo ka Kannywood ba, ka fake da ita ne kana diban ’ya’yan mutane kana hada su da iyayyen gidanka fasikai kana kashe aure kana cin amanar mutane da sukai maka sutura kana zagin mutanen da suka kyautata maka.

“Allah Ka raba mu da yin magana a kan abin da ba mu da masaniya a kai.”

– Abin da Adam A. Zango ya ce – 

Jarumi Adam A. Zango ya sake sanya hotonsa da bakin nasu, sannan ya ce, “Shan koko…”, sai Abubakar Bashir Maishadda ya mayar da martani cewa, “daukar rai faka-faka.”

– Shirin BBNaija –

Shirin BBNaija wani shiri da ake yi duk shekara, inda ake tara matasa maza da maza a cikin wani gida, karkashin jagoranci wani mai suna Biggie da ba a ganin shi, sai dai a ji muryarsa.

Ana cire mutane daya bayan daya, har zuwa ranar karshe da ake fitar mutum daya da ya zama zakaran shirin.

A shirin na bana, White Money ne ya zama gwarzo, inda ya samu da kyaututtuka da kimarsu ta kai Naira miliyan 90.

Shirin na samun suka musamman a Arewacin Najeriya, inda ake zargin shirin da nuna ‘fitsara’.

Daga cikin abubuwan da suka wakana a shirin na bana, akwai inda ake zargin wani mai suna Boma ya sadu da Tega, wadda matar aure ce.