✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hafsat Mohammed Baba: Jagoranci tun daga tushe

Hajiya Hafsat Mohammed Baba ta dade ana damawa da ita a gwagwarmayar kwato hakkin mata

Duk lokacin da mutum ya ziyarci ofishin Hajiya Hafsat Mohammed Baba zai samu mutane da dama, musamman yara da uwayensu, wadanda suka kawo mata kuka iri-iri.

Kuma duk da kasancewarta kwamishiniya, takan tsaya ta saurare su, ta kuma bi kadin koke-kokensu.

Hakan na faruwa ne, watakila, saboda Tauraruwar tamu ta jima tana fafutukar kare hakkin mata da yara, kuma har yanzu ba ta fasa ba.

Ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin an aiwatar da sauye-sauye a bangarori da dama da suka shafi kare hakkin mata da yara da ma nakasassu a Jihar Kaduna.

Hajiya Hafsat Mohammed Baba ta jagoranci fafutukar kawo sauyi a yadda ake kula da lamarin wadanda aka ci zarafinsu saboda jinsinsu da kuma amincewa da Dokar haramta Cin Zarafin Mutane a Jihar Kaduna.

Sannan ta taka rawa wajen kara yawan cibiyoyin kula da wadanda aka yiwa fyade a jihar.

Bugu da kari, bayan ta zama Kwamishinar Mata ta kafa wani asusu da ake kira KADSWEF mai samar da Naira miliyan 200 duk shekara don bayar da rance ga matan Jihar Kaduna su ja jari.

Fafutuka

A fafutukarta ta ganin an kare hakkokin mata ne a 2004 ta kafa kungiyar Global Initiative for Women & Children (GIWAC) mai kare hakkokin mata da yara a daukacin Kananan Hukumomin Jihar Kaduna.

Kafin nan Hajiya Hafsat Mohammed Baba ta yi aiki da Jami’yyar Matan Arewa (JMA) a matsayin shugabar makarantar Premier.

Sannan kuma ta rike mukamai da dama a matakin jiha da kasa a Majlisar Kungiyoyin Mata ta Kasa (NCWS). A yanzu haka ma ita ce Mataimakiyar Shugaba ta Kasa ta Uku.

Kujerun mata a siyasa

Da akwai mata da yawa irin su Hajiya Hafsat, da watakila matan Najeriya ba su nemi a yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima don ya tanadi wasu kujeru na musamman a gwamnati da jam’iyyun siyasa.

Domin kuwa ta rike mukamai daban-daban na jam’iyyun siyasa a matakai daba-daban, ciki har da Shugabar Jam’iyya reshen Jihar Kaduna.

Sannan ta rike mukamai na jam’iyyu daban-daban wadanda suka hada da Shugabar Mata, da Ma’aji a reshen Arewa maso Yamma na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa, da sauransu.

Hajiya Hafsat Mohammed Baba na cikin wadanda suka assasa kungiyar mata ’yan siayasa ta Women in Politics Forum; ita ce kuma Mataimakiyar Shugabar kungiyar mai kula da shiyyar Arewa.