✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haihuwa ta yi yawa a sansanonin ’yan gudun hijira — Zulum

Zinace-zinace da shan miyagun kwayoyi a sansanonin ’yan gudun hijira na karuwa.

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno, ya bayyana damuwa kan yadda ake ci gaba samun karuwar haihuwar jarirai a sansanonin ’yan gudun hijira.

Zulum ya ce hakan ke faruwa a sakamakon zinace-zinace da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi a sansanonin ’yan gudun hijirar a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Ya kuma sake jaddada matsayarsa ta bukatar sojin Najeriya su saurari shawarwari tare da riko da taimakon sojin ketare.

A cewarsa, haka zai taimaka wajen rubanya nasarorin da aka samu a fagen yaki da masu tayar da kayar baya a ’yan kwanakin nan.

Gwamnan ya ce akwai bukatar samun agaji daga sojojin haure kasancewar wadanda ake da su a kasar nan domin tunkarar masu tayar da kayar baya sun yi karanci.

Zulum wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas, ya yi furucin haka ne yayin wata hira da Gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

Aminiya ta ruwaito cewa, a hirar ce Gwamnan ya yi karin haske kan taron da kungiyar ta gudanar ranar Talata a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.