✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajj 2022: Dalilin rashin tashin maniyyata daga Filin Jirgin Jos

Filin jirgin saman da ke Jos ya yi wa jiragen da aka ba su jigilar alhazai kankanta.

Maniyyata aikin Hajjin bana daga Jihar Filato ba za su samu tashi daga Babban Filin Jirgi na Yakubu Gowon da ke Jos ba, zuwa Kasa Mai Tsarki.

Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Filato ta ce maimakon haka, za ta yi jigilar maniyyata ne daga Filin Jirgi na Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Sakataren Hukumar, Barista Auwal Abdullahi, ya bayyana wa wakilinmu a ranar Asabar cewa, “Ba zai yiwu a yi jigilar maniyyatan Jihar Filato ta Filin Jirgi na Yakubu Gowon da ke Jos ba a aikin Hajjin 2022.

“Dalili kuwa shi ne titin jirgin da ke filin jirgin na Jos ya yi wa manyan jiragen sama samfurin Jumbo Jet da aka ba su aikin jigilar maniyyata kankanta, don haka ba za su iya tashi ta Jos ba.”

Ya bayyana cewa, “Jirage masu daukar mutum 550 zuwa 600 ne aka bai wa aikin jigilar maniyyata a bana, kuma titin sauka da tashin jirgaren Babban Filin Jirgi na Jos ya yi musu kankanta.

“Duk da cewa filin jirgin ya kai matakin na kasa da kasa, amma yana bukatar a kara fadada shi yadda zai iya daukar manyan jirage; yanzu haka ana shirye-shiryen yadda Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya za ta zo a yi aikin.

“Ma’aikatar da Gwamnatin Jihar Filato sun samu fahimtar juna a kan dalilin da ba za a iya jigilar maniyyana daga filin jirgin ba a wannan karon.

“Gwamna Simon Lalong a shirye yake wajen ganin an yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da ganin alhazan Jihar Filato suna tashi daga filin jirgi na Jos; Idan Allah Ya yarda a 2023  daga filin jirgi na Jos alhazanmu za su tashi,” inji Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazan.