✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji 2022: Rukunin farko na maniyyatan Kano za su tafi Saudiyya ranar Litinin

A yanzu haka ma maniyyatan suna can a sansanin Alhazai na Jihar suna shirin tafiya.

Kimanin maniyyatan Jihar Kano 400 ne ake sa ran za su fara tashi zuwa kasar Saudiyya a yammacin Litinin din nan.

Babban Sakataren Hukumar Alhazan Kano, Alhaji Abba Danbatta ne ya bayyana hakan yayin da yake tattauna wa da manema labarai a birnin Dabo.

Aminiya ta ruwaito cewa maniyyatan da za su fara tashi a matsayin kashi na farko sun fito daga kananan hukumomin Kano guda shida da suka hada da Rano da Kibiya da Bunkure da Dawakin Kudu da Kura da Ajingi.

Abba Danbatta ya bayyana cewa Hukumar tasu ta gama shiri tsaf don fara jigilar maniyyatan a yau Litinin.

Ya kuma bayyana cewa “Idan har Allah Ya nufa abubuwa sun tafi kamar yadda aka tsara to maniyyatanmu za su fara tashi a yau din nan zuwa kasa mai tsarki, kuma jirgin Kamfanin Azman ne zai fara wannan aiki na jigilar.

“A yanzu haka ma maniyyatan suna can a sansanin Alhazai na Jihar.

“Daga yanzu zuwa kowane lokaci za a iya dibarsu zuwa filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano don tafiya zuwa kasa mai tsarki.”

Majiyar Aminiya daga Hukumar Alhazan Kano wacce ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa, an samu tsaiko na jigilar maniyyatan jihar ne sakamakon ’yar matsala da ta taso tsakanin Hukumar da kuma Kamfanin Jiragen na Azman.

“Sai dai a yanzu an warware wannan matsala don haka a yanzu za a fara jigilar maniyyatan a yau Litinin idan Allah Ya yarda,” a cewar majiyar.