✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji: An fara rajistar maniyyatan 2023 a Saudiyya

Saudiyya ta lashe amanta kan yin riga-kafin COVID-19 ga maniyyata aikin Hajjin 2023

Ma’aikatar Aikin Hajji da Umarah ta kasar Saudiyya ta fara yi wa maniyyata aikin Hajji a shekarar 2023 da muke ciki rajista a ranar Alhamis.

Sai dai a wani mataki mai kama da mi’ara-koma-baya, gwamnatin Saudiyya ta dawo da sharadin kammala allurar riga-kafin COVID-19 ga maniyyata aikin Hajji na bana.

Ma’aikatar ta ce wajibi ne maniyyatan kasar su kammala daukar allurar riga-kafin COVID-19 da sauransu akalla kwana 10 kafin ranakun fara aikin Hajji.

Hakan kuwa na zuwa ne bayan a kwanakin baya ma’aikatar ta shaida wa Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) cewa ta soke dokar kammala daukar allurar riga-kafin COVID-19 ga maniyyata.

Kamfanin Dillancin Labaran Saudiyya (SPA) ya ruwaito gwamnatin kasar ta jaddada soke soke tafiya da muharrami namiji ga mata maniyyata.

Ma’aikatar ta kuma bullo da sabon tsarin adashin gata ga maniyyatan kasar masu karamin karfi a kan Riyal 3,984.

A karkashin sabon tsarin adashin gatan, maniyyata masu karamin karfi za su iya yin zubi sau uku domin samun damar Sauke farali, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Saudiyya (SPA) ya ruwaito.

Ta bayyana cewa mafi karancin shekarun maniyyata masu neman gurbi ta intanet shi ne 12, sannan za a ba da fifiko wajen rabon kujeru ga maniyyatan 2022 da ba su samu zuwa ba, sannan wadanda suka fara cika kudin kujerarsu a bana.

Ta kuma shawarci maniyyata su tabbata sun yi rajista ta hannun kamfanoni masu lasisi domin guje wa ’yan damfara.