✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajjin 2023: Za a fara jigilar maniyyata a watan Mayu —NAHCON

Hukumar ta ce tana so ta kammala shirye-shiryenta a kan lokaci don kaucewa samun matsala.

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON), ta ce za ta fara jigilar maniyyatan 2023 zuwa Kasar Saudiyya a ranar 21 ga watan Mayu, 2023.

Shugaban hukumar, Alhaji Zikrullah Hassan, ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da kwamitin sanya ido kan harkokin sufurin jiragen sama na hajjin bana a ranar Laraba a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya bayar da rahoton cewa, kamfanonin jiragen sama 10 ne suka nemi sahalewar jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya don gudanar da aikin hajjin shekarar 2023.

Kamfanonin da suka nuna sha’awarsu sun hadar da Aero Contractors, Air Peace, Arik Air, Flynas, Azman Air, Max Air, Sky Power, United Nigeria Airlines.

Ragowar sun hada da Cargo Zeal, Cargo Solo Deke Global Travels.

Shugaban NAHCON ya bukaci kwamitin tantancewar da su yi aiki tukuru tare da gabatar da rahotonsu kafin ranar 7 ga watan Maris, domin mika wa Shugaban Kasa kasa Muhammadu Buhari don amincewa.

Ya kuma bukaci kwamitin da ya tabbatar da cewa an warware duk wata matsala ta fasaha da ta shafi jiragen sama a kan lokaci.

Kazalika, Hassan ya shawarci dukkan maniyyatan da su kammala rajista da hukumomin jin dadin Alhazai na jihohinsu a kan lokaci.

A cewarsa, za a rufe rajistar aikin hajjin 2023 a kan lokaci don cika wa’adin da gwamnatin Saudiyya ta kayyade.

Tun da farko, Alhaji Abdullahi Hardawa, shugaban kwamitin tantancewar kuma Kwamishinan Ayyuka na NAHCON, ya bayyana kudurinsa na yin aiki tukuru domin ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajjin 2023.

Har ila yau, Sanata Adamu Bulkachuwa, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai Kula da Harkokin Kasashen waje, ya bukaci mambobin kwamitin tantancewar da su tabbatar sun yi aikin da ya dace

“A matsayina na Shugaban Majalisar Dattawa kan Harkokin Kasashen Waje, kullum muna sanya ido kan yadda ake gudanar da aikin Hajji.

“Idan kamfanonin jiragen sama sun yi aiki mai kyau, za a samu nasara jigilar maniyyata.

“Ina kira a gare ku da ku hada kan ku don tabbatar da da ba a samu matsala ba.”