✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajjin Bana: An yi wa maniyatan Yobe rigakafin COVID-19

Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Yobe, Bukar Kime, ya ce an yi wa kusan duk maniyyata aikin Hajjin bana daga jihar allurar…

Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Yobe, Bukar Kime, ya ce an yi wa kusan duk maniyyata aikin Hajjin bana daga jihar allurar rigakafin COVID-19.

Ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Aminiya ta wayar salula.

Sannan ya ce an fara bita don wayar da kan maniyyatan duk da cewa har yanzu ba su samu cikakken bayani na yadda za a gudanar da aikin ibadar ba.

Dadin dadawa, ba a tabbatar wa kowace jiha da adadin kujerun da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ware mata ba.

Sakataren ya ja hankalin maniyyata su tabbatar da kiyaye dokoki da ka’idoji da aka gindaya na kariya daga cutar ta COVID-19 musamman wajen yawaita wanke hannu da sanya takunkumi.