✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajjin bana: Maniyyatan Najeriya 2,009 sun isa Madina

A bana dai maniyyata 43,000 ne za su sauke farali daga Najeriya

Akalla maniyyata Aikin Hajji 2,009 ne daga cikin 43,000 da aka ware wa Najeriya suka isa birnin Madina na kasar Saudiyya tun bayan fara jigilarsu a shirye-shiryen aikin a bana.

A wannan shekarar dai, maniyyata miliyan daya ne ake sa ran za su sauke farali daga kasashen duniya daban-daban.

Jihohin da suka riga suka fara tashi daga Najeriya su ne na Borno da Nasarawa da kuma Babban birnin Tarayya Abuja.

Maniyyatan dai kan ziyarci birnin na Madina don yin ziyara da sallah a masallacin Annabi Muhammad (S.A.W), ko dai kafin ko kuma bayan kammala Aikin Hajjin.

Yin sallah a masallacin na da falala fiye da sau 1,000 wajen yin sallar fiye da wadda aka yi a kowanne masallaci a fadin duniya, in ban da Masallaci Harami da ke birnin Makkah.

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) dai ta tura kwamitoci da dama, da suka hada da na yada labarai da na lafiya da na samar da masaukai da kuma na kudi da na aikace-aikace don saukaka wa alhazan zamansu a kasar mai tsarki.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa tuni maniyyatan suka fara sauka a masaukansu da ke kusa da Masallacin Harami na Makkah, kuma akasari otal-otal din da aka tanadar musu na kusa da Masallacin.

Sama da maniyyata miliyan biyu ne kan ziyarci dakin Ka’aba don gudanar da Aikin Hajji a kowacce shekara, kuma ana yin ibadar ne a watan 12 na shekarar Musulunci wato Zul-Hijjah. (NAN)