✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajjin bana: Rukunin karshe na Alhazan Kwara sun iso Najeriya

Alhazan sun iso gida Najeriya da misalin karfe 1 na dare

Jirgi dauke da rukunin karshe na alhazan Jihar Kwara da suka yi Aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya sun isa Ilorin, babban birnin jihar da safiyar Laraba.

Alhazan da adadinsu ya kai 328 tare da jami’an Hukumar Alhazai ta Jihar da suka hada da shugaban hukumar, Dokta Abdulkadir Sambaki, sun isa filin jirgin a jirgin sama na kamfanin Max Air da misalin karfe 1:17 na dare.

Da yake jawabi bayan saukar jirgin, Dokta Abdulkadir Sambaki, ya gode wa Allah da ya sa aikin hajjin ya samu nasara.

Sambaki, ya kuma gode wa Gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq, bisa goyon bayan da ya bai wa hukumar a tsawon lokacin aikin hajjin.

Ya bayyana jin dadinsa da cewa babu wani abu da ya faru da mahajjatan jihar a kasar Saudiyya tare da gode musu da kasancewa jakadu na gari.

Mutum biyu daga cikin alhazan, Hajiya Sherifat Shade AbdulKareem da Hajiya Ramata Bukola Olesin, sun bayyana aikin hajjin da cewa ya sami gagarumar nasara.

Sun bukaci ’yan Najeriya da su ci gaba da yi wa kasa addu’a domin ta shawo kan dukkan kalubalen da take fuskanta.